A yau Talata da misalin karfe 10 na safe ne ‘yan sanda suka rufe kasuwar Wuse dake babban birnin tarayya Abuja, sakamakon wata hatsaniya da ta barke tsakanin magoya bayan shugaba Buhari da masu zanga-zangar Buhari ya sauka karkashin jagorancin mawaki CharlyBoy.
Hatsaniyar ta fara ne yayin da masu zanga-zangar suka fara rera take suna neman shugaba Buhari ya dawo ko ya sauka daga mulkin kasar, sai magoya bayan Buhari da suke kasuwar suka fito suna kalubalantar masu zanga-zangar suna cewa ‘karya kuke’ bazai sauka ba.
Hakan ya jawo rikici tsakanin masu zanga-zangar, jami’an ‘yan sanda masu kwantar da tarzoma sun tarwatsa duk magoya bayan biyu da ruwan zafi daga bisani suka sallame kowa domin rufe kasuwar ta Wuse.