Connect with us

KASASHEN WAJE

Rikici Ya Hallaka Mutane Da Dama A Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya

Published

on

Tashe-tashen hankula tsakanin kungiyoyin tsageru masu dauke da makamai sun janyo mutuwar kusan mutane 40 a yankin Arewacin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

Kimanin mutane 25 sun hallaka sakamakon artabu tsakanin kungiyoyi masu dauke da makamai a garin Ndélé na arewacin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

Wasu majiyoyi sun bayyana wadanda lamarin ya ritsa da su sun kai kusan 40. Galibin wadanda rikicin ya shafa sun kasance fararen hula.

Dakarun kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya sun gaza samar da zaman lafiya tun shekara ta 2013 bayan kifar da gwamnatin Shugaba François Bozizé da ‘yan tawaye suka yi.

A cewar Majalisar Dinkin kimanin rabin al’umar kasar ta Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya suna dogara kan agajin abinci kimanin mutane milyan 2.6.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: