Wasu masu kishin cigaban karamar hukumar Kankia sun bayyana cewa rikicin da ya ta so a cikin jam’iyyar APC na karamar hukumar babu abinda ya hada shi da kyakkyawar danganatar da ke tsakanin Ahmed Musa dangiwa shugaban ‘Mortgage Bank’ da kuma Sanata Ahmad Babba Kaita
Wannan bayanin yana fitowa ne kwana daya da jam’iyyar APC a matakin jaha ta yi wani taro a Katsina inda ta bayyana cewa an yi taron ne bisa umarnin shugaban kasa Muhammadu Buhari na dinke duk wata baraka da ke cikin jam’iyyar.
To sai dai mutane irin su Dakta Abdullahi Nuhu Kafin Soli daya daga cikin masu ruwa sa tsaki na jam’iyyar APC a karamar Hukumar Kankia yana cewa wannan rikicin da ya ta so abu na cikin gida babu ruwansa da alakar da ke tsakanin Ahamd dangiwa da Sanata Babba Kaita.
“Darbarwar da ke faruwa acikin jam’iyyar APC a Kankia wanda ta yi sanadiyar cire shugaban jam’iyyar na kararmar hukumar Kankia, Alhaji danjuma Mamman Rimaye, abu ne da ya shafi harkar jam’iyyar kuma shuwagabannin jam’iyya su ke da hankalin daukar wannan mataki kuma sun dauka” inji shi
Dakta Kafin Soli ya kara da cewa wannan mataki sun dauke shi ne saboda irin matalolin da shugaban ya ke kawo ma jam’iyyar da kuma irin illar da ake hangen zai haifar nan gaba, wannan yasa aka dakatar da shi kuma suka bukaci da ayi bincike akan zargin da ake yi masa daga uwar jam’iyyar ta jiha.
Kazalika ya bayyana cewa hakkin shuwagabannin na jiha ne su duba duk wani korafi da aka kawo gabansu domin yi wa kowa adalci, domin a cewarsa haka shugaban kasa Muhammadu Buhari yake, amma matsalar shi ne an yanke hukuncin da bai yi wa mutanen Kankia dadi ba, domin dai kamar yadda suka ambata Kankia abu daya.
Dakta Abdullahi Kafin Soli ya yi kira ga uwar jam’iyyar ta jiha da su girmama matakin da mutanen Kankia suka dauka na dakatar da shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar, Alhaji danjuma Maman domin cigban jam’iyyar APC a Kankia kuma hakan zai tabbatar da adalci irin wanda shugaban Buhari yake maganar ayi
Shima da yake karin bayani dangane da wannan sa-toka-sa-katsi ta jam’iyyar APC da ta kunno kai a karamar hukumar Kanki a daidai lokacin da ake ta kokarin ganin an dinke barakar da ke cikin jam’iyyar domin tunkarar kalubalen da ke gaban jam’iyyar a mataki na kasa, Ali Jimi ya yi karin haske
Alhaji Aliyu Muhammad wanda aka fi sai da Ali Jimi cewa yake “ina kira da babar murya ga shugaban jam’iyya na jiha, Alhaji Shitu S. Shitu da cewa al’amarin siyasa na mutane ne, kuma da mutane ne ake amfani a samu duk abinda ake bukata na rabo acikin siyasa.”
Ya ce matakin da mutanen kankia suka dauka na dakatar da shugaban jam’iyyar APC na Kankia, Alhaji danjuma Mamman daga mukaminsa, duk da ance uwar jam’iyya ta jiha ta maido shi daga dakatarwa, har wala yau an sake dakatar da shi, sannan sun rubuta a rubuce zuwa ga duk wani mai ruwa da tsarki da kuma uwar jam’iyya ta jiha domin duba koken da kuma daukar mataki na adalci.
“Inaso mutane su gane cewa shi zalunci bai dawwama, adalci ne ke dawwama, kuma jam’iyyar APC ba ta mutun daya ba ce, ta kowa da kowa ce, jam’iyya ce ta adalci wanda ke neman nasara a Najeriya baki daya, kuma ta yi sa’a da shugaba jagora Janar Muhammadu Buhari” inji Ali Jimi
A cewarsa abinda suka yi tsammani shi ne uwar jam’iyya ta jiha zata dauki mataki game da koken da aka gabatar mata, amma sai wasu suka alakanta wannan rikici da cewa yana da nasaba da shugaba kuma jagora na wannan tafiya a garin Kankia ARC. Ahmad Musa dangiwa, wanda ko kusa baya da alaka ko masaniya da wannan rikici.
Ali Jimi ya kara da cewa Arc Ahmad dangiwa Da Sanata Ahmad Baba Kaita suna da kima da mutunci a idon mutanen Kankia, har yanzu ana mutunta su ana girmama su kuma shuwagabanni a karamar hukumar Kankia.
Daga karshe dai Ali Jimi ya yi kira da baban murya ga shugaban jam’iyyar APC Malam Shitu S. Shitu da ya duba wannan lamari kuma a dauki matakin da ya da ce, haka kuma ya yi kira ga gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari da ya sa baki wajan ganin abubuwa sun daidaita a tafiyar jam’iyyar APC ta Kankia