Connect with us

RIGAR 'YANCI

Rikicin APC: Buhari Bai Saba Dokar kasa Ba – Shugaban Kungiyar Gwamnonin APC 

Published

on

A jiya ne Gwamnan Jihar Kebbi kuma Shugaban kungiyar Gwamnonin APC, Sanata Abubakar Atiku Bagudu, ya bayyana cewar, gudanar da taron shuwagabannin jam’iyyar APC da wasu gwamnonin jam’iyyar tare da Shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar ta APC da su ka gudanar a cikin makon da ya gabata babu inda ya saba wa dokar kundin tsarin mulkin kasa.

Gwamnan jihar ta Kebbi ya bayyana hakan ne yayin da ya ke amsa tambayoyin manema labarai kan matsalar rikicin jam’iyyarsa ta APC a matsayinsa na Shugaban Kungiyar Gwamnonin Cigaban Jam’iyyar APC a Birnin-kebbi, babban birnin Jihar Kebbi, a jiya.

Ya cigaba da cewar, “a matsayin shugaban Buhari dan jam’iyyar APC wanda kuma ya yi takarar kujerar shugabancin kasar Nijeriya a karkashin jam’iyyar ta APC a kundin tsarin jam’iyyar APC ya na da damar da zai halarci taron tattaunawar jam’iyyar, haka kuma ya na da iko a matsayinsa na shugaban kasa ya kira ‘ya’yan jam’iyyarsa don tattaunawa ko yanke hukunci idan wata matsala ta taso a cikin jam’iyyarsa ta APC.

“Saboda haka tun da kundin tsarin jam’iyyar APC ya bashi damar yin hakan, don haka bisa ga tsarin jam’iyyarsa babu idan ya sabawa dokar kundin tsarin mulkin kasa ko na jam’iyyar APC.

Bugu da kari ya ce ” taron tattaunawar APC na gaggawa aka gudanar don dakile matsalolin shugabancin jam’iyya da ke addabar APC a matakin kasa da kuma na wasu Jahohin kasar nan, bisa ga hakan ne aka gudanar da wannan taron tattaunawar na gaggawa da wasu ‘yan adawa ke maganar cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sabawa dokar kundin tsarin mulkin kasa, wanda babu gaskiya a cikin maganganun da su ke fadi”.

Hakazalika ya ce ” bisa ga wadanda hujojin maganar cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya saba doka ba gaskiya ba ne domin a matsayarsa na dan jam’iyyar APC kuma Shugaban kasar Nijeriya a karkashin wannan jam’iyyar ta APC yana iya kiran taron tattaunawa na jam’iyyarsa ko ya halarta da kuma damar daukar duk wani hukunci ga duk wani dan jam’iyyar APC da ya saba kundin tsarin mulkin jam’iyyar, a cewar Gwamna Bagudu”.

Har ilayau ya cigaba da kara bayyana cew” taron tattaunawar APC da shugaban Muhammadu Buhari ya gudanar na walwale matsalolin da ke cima jam’iyyarsa tuwo a kwarya da Jama’ar kasa ke ta tsokaci a kai, saboda hakan ne Shuwagabannin jam’iyyar da wasu gwamnonin na jam’iyyar suka zauna bayan kammala taron tattaunawar na majalisar zartarwa ta gwamnatin Tarayya wanda dukkansu manyan jigajigan jam’iyyar APC ne, Inji Gwamna Bagudu”.

Saboda haka ya ke kara kira ga ‘yan uwansa gwamnonin jam’iyyar APC da su kara zage damtse wurin ganin cewar ” dukkan barakar da ke akwai a tsakanin ‘ya’yan jam’iyyarsa ta kare.

Daga nan kuma ya nemi mambobin jam’iyyar ta APC a duk jahohin kasar Najeriya su ci gaba da baiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma sauran masu mulki a karkashin jam’iyyar APC don kara samar da ci gaba mai amfani ga al’ummar kasar Najeriya baki daya. Haka kuma ya ce ” zaben gwamnonin Jahohin Edo da Ondo jam’iyyar APC zata lashe jahohin biyu domin sun ci gajiyar dimokradiyya a wadannan yankunan biyu na kasar nan”.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: