Rikicin Binuwai: Al-Makura Ya Yafe Wa Ortom

Gwamnan Jihar Nasarawa, Umaru Tanko Al-Makura, ya ce, da shi da sauran jama’ar Jihar sun yafewa takwararsa na Jihar Binuwai, Samuel Ortom, kan zargin da gwamnan na Jihar Benuwai ya yi wa Jihar cewa tana boye wadanda suke kai hare-hare a yankunan Benuwai, a kauyen Tunga da ke Karamar Hukumar Awe a Jihar ta Nasarawa.

Gwamna Al-Makura, ya bayyana yin yafiyar ce a lafiya fadar gwamnatin Jihar, a lokacin da ya karbi bakuncin tawagar kamfanin Dangote, wadanda su ka zo Jihar domin jajintawa al’ummar jihar kan abin da ya faru a Jihar Benuwai, wanda kuma ya sanya Jihar karbar bakuncin ‘yan gudun hijira daga Jihar Benuwai.

Gwamna Al-Makura, wanda ya jajantawa al’ummar Jihar Binuwai kan abin da ya same su ya ce, Jihohin Nasarawa da Binuwai abu guda ne, kuma duk abin da ya samu daya tamkar dukkan su ne, inda ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici.

Gwamnan ya ce, har cikin zuciyarsa ya yarda da afuwar da takwararsa Ortom, ya nema kuma ya yafe masa har ga Allah kan kalamun da ya furta a kan Jihar Nasarawa game da rikicin Jihar Benuwai.

Ya kara da cewa, zai ci gaba da hada kai da Gwamnan na Jihar Benuwai wajen tabbattar da tsaro, mussamman a kan iyakokin Jihohin su, kuma ba zai ja da baya ba a taimakon da yake yi wa ‘yan Jihar Benuwai masu zaman gudun hijira a Jihar Nasarawa.

Gwamna Al-Makura, ya godewa Shugaba Muhammadu Buhari, kan matakin da ya dauka na tura karin jami’an tsaro a yankunan da ake rikicin, yana mai cewa ko a kwannan nan rundunar ‘yansanda kwantar da tarzoma biyar ne aka turo su yankunan da suke da kalubalen tsaro a Jihar.

Haka nan Gwamna Al-Makura, ya bukaci mazauna Jihar da su rika daukar batun tsaro da mahimmanci ta hanyar marawa hukumomin tsaro a Jihar domin karfafa masu gwiwa a aikinsu.

A na sa bangaren, daya daga cikin manyan manajojin kamfanin Dangote, wadanda ya jagoranci tawagar, Abdullahi Sule, ya ce tawagar ta kasance a Jihar ne domin ta jajantawa al’ummar jihar kan abin da ya faru.

 

Exit mobile version