Connect with us

LABARAI

Rikicin Filato: Ba Fulani Ke Kashe-Kashe Ba –MACBAN

Published

on

Rikicin Filato: Ba Fulani Ke Kashe-Kashe Ba –MACBAN
Kungiyar makiyaya ta Miyetti-Allah ta Nijeriya ta yi Allah-wadai da rikicin da ya afku a wasu kananan hukumomi guda uku da ke jihar Filato, inda aka kashe mutane masu yawa tare da asarar dukiyoyi na miliyoyin Naira.
Sakataren kungiyar na kasa Baba Othman Ngelzarma, ne ya bayyana haka lokacin da suke zantawa da wakilinmu a jiya, ya ce dole ne dukkan mai son ci gaban kasar nan, ya yi Allah-wadai da wannan rikici.
Sannan ya nesanta kungiyar ta su da wata kungiya mai suna “Kungiyar Fulani masu Neman ‘yanci ta kasa” wanda ya ce wannan kungiya ce wadda ba ta da asali, kuma ya ce ta fito da wata sanarwar da za ta kara dagula zaman lafiyar da ake yi da makiyaya.
“Saboda haka muna daxa tabbatarwa da al’umma cewa, ba mu san wananan kungiyar ba a Nijeriya”. Kuma bisa dukkanin alamu an kirkro wannan kungiya ce domin a kara rura wutar rikicin jos. Saboda haka ya kamata gwamnati ta gudanar da bincike a kan wannan kungiya, domin ta haka ne za a gano masu yin kalaman da za su kara rura wutar rikici a tsakanin al’ummar Nijeriya “, in ji Baba Othman.
Haka kuma ya roki gwamnati da ta yi a dalci wajen gudanar da bincike kan wannan rikici, sannan kuma a gaggauta kai wa waxanda rikicin ya rutsa da su taimako.
“Kungiyar Miyetti-Allah ta mika sakon jajenta ga al’ummar jihar Filato, musamman iyalan waxanda rikicin ya rutsa da su da kuma gwamnan jihar Honarabul Simon Bako Lalong, wanda duk tsawon shekara ukun da share yana mulki yake ta kokarin tabbatar da zaman lafiya. Haka kuma, kungiyar ta jinjina wa gwamnatin tarayya bisa tura jami’an tsaro na musamman yankunan da rikicin ya faru domin tabbatar da zaman lafiya “,in ji shi.
Daga nan kuma sai ya nuna cewa kungiyar ta su ta damu matuka kan yadda wasu suka rusa ginin da aka daxe ana yi na haxin kai tare da fahimtar juna a wannan kasa.
Saboda haka kuma sai ta sake kira ga gwamnati da ta tabbatar an hukunta dukkan waxanda aka kama kuma suke da hannu a kan afkar da wannan tarzoma.
Sannan kuma ya ce, kungiyar ta yi maraba da yunkurin da gwamanatin tarayya ke yi na gyara harkokin kiwo a kasar nan, wanda kuma zai rage rikice-rikicen da ke faruwa tsakanin makiyayay da manoma. Haka kuma ya bukaci sauran al’umma da su bayar da gummawar da za su iya wajen ganin an kawo karshen ire-iren waxannan rikice-rikice na tsakanin Fulani da manoma.
Sannan ya tir da yadda wasu bata-gari ke datse hanyoyin mota da zarar wani abu ya faru su ci gaba da kashe matafiya. Ya ce, kungiyarsu, kungiyar makiyaya ce da ba ta taba amincewa da a kai wa wani hari ba. Saboda haka sai ya bukaci al’umma su zauna lafiya kuma su ci gaba haxa kansu.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: