Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home RAHOTANNI

Rikicin Gine Masallacin Idi A Kano: Ali Baba Ya Warware Zare Da Abawa

by Tayo Adelaja
October 24, 2017
in RAHOTANNI
3 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Abdullahi Muhammad Sheka, Kano

Tun bayan ɓullar aniyar Gwamnatin Kano na yunƙurin gina rumfunan Kasuwanci a zagayen filin Masallachin Idi dake Ƙofar Mata a cikin birnin Kano, ake ta faman ya mutsa gashin baki tsakanin al’umma,  musamman ganin a baya anyi ƙoƙarin mayar da filin idin wurin ajiye motoci da baburan ‘yan Kasuwar dake zagaye da masallachin irinsu kasuwar Kantin Kwari da kuma Ƙofar Wambai. Yanzu kuma sai aka ji Gwamnati ta gama shiri tsaf na samar da rumfuna wanda aka tsara zasu zagaye filin baki ɗaya.

Tunda farko Gwamnatin Kano ta shelanta yin wannnan gine gine jama’a suka nuna rashin amincewarsu, wanda daga baya malamai suka sanar da nasu matsayin inda suka nuna rashin da cewar gina rumfuna Kasuwa awani ɓangare na masallachin Idin. Kuma alhamdulillahi Gwamnatin ta karɓi wannan kira nasu ta dakartar da wannan aiki a wancan lokacin. Amma daga baya wasu mutune dake ganin yin hakan zai taimaka wajen samar da tsaro a filin wanda a shekara sau biyu kacal ake salla acikinsa, kuma ana ganin yadda wasu ɓata gari kan shiga harabar Masallachi domin yin kashi da kuma shaye shayen miyagun kwayoyi, saboda haka su ke ganin idan aka samar da waɗannan rumfuna za’a samu sauƙin wannan baɗala.

Alhaji Ali Baba Fagge shi ne mashawarci na musammankan harkokin addini ga mai girma Gwamna Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya yiwa wannan matsalar kallon tsanaki tare da warware zare da bawar ƙulle ƙullen dake cikin kyakkyawan shirin na gwamnati a cewarsa. Ya ce ba wai a Kano ne aka fara gina shaguna da suka zagaye wani masallachi ba, hatta masallachin Ka’aba akwai manyan manyan shaguna harma da otal otal wanda ake gudanar da ciniki a cikinsu.  Ya bayar da misali da Kasuwa zam zam, Mai agogo shima Ka’aba yake Kallo duk ba’a yi aka yarda da yin waɗancan inji Ali Baba Fagge? Haka masallachin Madina akwai Ɗaiba, Darul-taƙwa otan ne babba ga kuma wuraren sayar da gwala gwalai ana sayarwa duk suna kallon masallachin Annabi (SAW).

Hakazalika Ali Baba Fagge ya bayyanawa masu wancan tsegumi cewar bafa masallachin Idi baki ɗaya za’a gine ba, masallachin faɗin mita dubu ne dashi abinda za’a cira shi ne mita goma, mita shida tsayi mita huɗu faɗin shagon, haka ake buƙaatar zagaye Masallachin kuma ko wane mai kanti zai sa fitila ta haske cikin filin masallachin domin samar da tsaro, kuma filin Idi na nan ba zaka gane cewa ma an taɓa filin ba. Yace harma tsarota mutane ake wai idan wata gwamnati ta dawo zata kwace to kai Allah ne kasan wanda zai dawo, kawai Kwankwaso don Allah ya dawo da kai sai ka ɗauka zaka iya dawo da wani. Ko ma’aha da aka rushe ta ai hassada ce da ƙyashi inji Ali Baba Fagge.

 

 

SendShareTweetShare
Previous Post

Mata Sama Da Dubu Ke Aikin Ciyar Da Ɗalibai A Bauchi –Soro

Next Post

Babu Cutar Ƙyandar Biri a Nasarawa

RelatedPosts

Tuhumar Malam Abduljabbar Za A Yi, Ba Mukabala Da Shi Ba– Sheikh Khalil

by Sulaiman Ibrahim
11 hours ago
0

Daga Nasir S. Gwangwazo, Abuja Shugaban Majalisar Malamai na Shiyyar...

ISWAP

Boko Haram Ta Yi Garkuwa Da Ma’aikatan Jinkai Bakwai A Dikwa

by Sulaiman Ibrahim
11 hours ago
0

Daga Muhammad Maitela, Maiduguri A harin bayan nan da mayakan...

Makanike

Shari’ar Gonaki: Kotu Ta Aike Wa Rundunar Soja Da Ma’aikarar Shari’a Sammaci

by Sulaiman Ibrahim
11 hours ago
0

Daga Isa Abdullahi Gidan ‘Bakko, Zariya Kotun daukaka kara dake...

Next Post

Babu Cutar Ƙyandar Biri a Nasarawa

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version