Daga Rabiu Ali Indabawa,
Rikicin hana sanya hijabi a wasu makarantu mallakin kungiyoyin addinin Kirista a Jihar Kwara ya munana da safiyar Laraba yayin da Kiristoci suka nuna rashin amincewarsu da umarnin gwamnati.
A karo na biyu, gwamnatin jihar ta kulle makarantun, domin kwantar da kurar, amma a daren Talata, Kwamishanar Ilimin Jihar, Kemi Adeosun, ta sanar da umarnin bude makarantun.
Majiyarmu tattaro cewa, yayin da dalibai suka koma makaranta da safiyar Laraba, an hana su shiga, saboda malamai Kiristoci da shugabannin makarantar sun fara gudanar da zanga-zanga na nuna rashin amincewa.
An samu labarin cewa rikici ya barke a makarantar Baptist dake Surulere kafin ‘yan asalin garin suka kwantar da kurar. Har yanzu gwamnatin Jihar Kwara ba ta yi jawabi kan lamarin ba.
A daren jiya, gwamnatin ta saki jawabin ba da umurnin bude makarantu.
“Gwamnati ta gamsu cewa dokar da ta kafa na bai wa dalibai Musulmai damar sanya Hijabansu zuwa makaranta zai tabbatar da zaman lafiya da fahimtar juna,” a cewar Kwamishanar Ilimin Kwara, Kemi Adeosun.