Daga Muhammad Shafi’u Saleh, Yola
Kungiyar Igbo mazauna jihar Adamawa (Igbo Cultural Association, Adamawa) sun yaba da kokarin da sukace gwamnatin jihar ta yi na tabbatar da zaman lafiya da kare musu dukiyoyi a jihar.Dama dai gwamnatin jihar ta basu tabbacin tsaro da zaman lafiyar ne biyo bayan tashin hankali da hare-hare kan ‘yan Arewa mazauna Kudu maso-gabashin kasar ke kai musu, sakamakon batun raba kasar da ‘yan kungiyar IPOB ke yi.
Da ya ke magana a wani taron manema labarai a Yola sarkin kungiyar Igbo mazauna jihar Cif Fidelis Umeh, ya ce, sun gana da gwamnan jihar Umaru Bindow a lokuta da dama inda gwamnan ya muna musu sauna da basu tabbacin zaman lafiya.Ya ce irin matakan tsaron da gwamnatin jihar ta dauka biyo bayan faruwar abun bakin cikin da ya haifar da rashin hankali a kasar, abun a yaba ne da nuna farinciki.”Zan yi amfani da wannan dama, domin na bayyana gamsuwa da farincikimu ga gwamnatin Umaru Bindow, bisa wannan ci gaba daaka samu.
Ina kara yiwa gwamna godiya bisa tabbacin da ya baiwa Igbo mazauna jihar Adamawa tsaro da zaman lafiy” inji Umeh.Ya ci gaba da cewa: “Mu mutanen Igbo a Adamawa mun gamsu mun kuma yarda cewa Adamawa babu wani abu na shirin auka wa tsirarun kabilu saboda banbanci yare. Shugabannin Igbo mazauna Adamawa muna kira ga daukacin ‘yan’uwanmu a jihar bakidaya da su zauna lafiya su ci gaba da harkokin kasuwancinsu” inji Umeh.