Yusuf Shuaibu" />

Rikicin Iyaka Ya Ci Rayukan Mutum Uku A Kuros Ribas

An bayar da rahoton mutuwar mutum uku, a wani rikicin da ya barke a tsakanin ‘yan kauyen Ikot Osute da kuma ‘yan kauyen Ikot Ukpong da ke cikin karamar hukumar Oruk Anam ta Jihar Akwa Ibom. An bayyana cewa, rikicin ya fara ne lokacin da wata mata mai suna Ime Etuo, ta samu rashin jituwa tsakanin ta da mijinta, inda ta koma gidan mahaifinta da ke kauyen Ikot Osute. Amma daga baya sai su ka shirya da mijin nata, sai su ka koma gidan mahaifinsa da ke cikin kauyen Ikot Ukpog. Bincike ya nuna cewa, Ime Etuo ta sa matasan kauyen Ikot Osute, wanda Udeme ya ke jagoranta da su bugi mijin nata har sai da ya mutu.

A cewar wani wanda lamarin ya afku a gaban idanunsa mai suna Idongesit Jacob, “basaraken kauyen Ikot Osute, Cif Tana, ya sa matasa sun tsare wadanda su ka kashe mutumin kafin ya kira ‘yan sanda. “Lokacin da a ke jiran ‘yan sanda, sai Udeme ya yaudari mazauna kauyen a kan ya na jin yunwa, su kwance shi ya ci abinci. Ana kwance ijiyar da a ka daure Udeme, sai ya tsare zuwa cikin daji. Matasa sun yi kokarin neman sa amma ba su ganshi ba.”

Ya bayyana cewa, lokacin da matasan kauyen Ikot Ukpong, wato matasan kauyen mamacin su ka samu labarin cewa, an kashe musu dan uwa, sai su ka kawo farmaki zuwa cikin kauyen Ikot Osute. Jacon ya kara da cewa, farmakin ya yi tsanani sosai, inda ta kai ga harbe wata mata mai suna Idongesit Bassey, har lahira, yayin da a ka jikkata mutum biyu, inda a ka garzaya da su zuwa babbar asibiti Immanuel domin yin jinya. Ya ce, daga baya daya daga cikin wadanda a ka kai asibiti mai suna Promise Unananowo ya mutu, domin asibitin ba su da na’urar cire harsashi, yayin da a ka kai shi wajen likitan gargajiya domin a cire masa harsashin.

“Mun dauke shi tun daga babbar asibitin Immanuel zuwa wurin likitan gargajiya domin a cire masa harsashi, ya dai mutu ne lokacin da a ka kammala cire masa harsashin sakamakon kin yin fitsari.”

Ya ce, sakamakon haka ya sa wadanda su ka mutu a wannan farmaki sun k aru daga biyu zuwa uku, yayin da mazauya kauyen su ke ta gudu zuwa makwabtar yankin.

A halin yanzu dai, kakakin rundunar ‘yan sandar Jihar Akwa Ibom, SP Odiko Macdon, ya tabbatar da wannan farmakin. Ya bayyana cewa, ‘yar sanda su na farautar wadanda su ke da hannu a cikin wannan lamari tare da kokarin cafke su, domin a gurfanar da su a gaban kuliya.

Exit mobile version