Connect with us

MANYAN LABARAI

Rikicin Jam’iyya: Babu Da-na-sani A Shugabancin APC Da Na Yi—Oshiomhole

Published

on

Tsohon Shugaban jam’iyyar APC, Adams Oshiomhole, ya bayyana cewa, ya rungumi kaddara a tsige shi tare da ‘yan kwamitin gunawar jam’iyyar da kwamitin zartarwar jam’iyyar ta yi,ya kuma ce, bai yi kuma dana sanin shugabancin jam’iyyar day a yi ba gaba daya.

A ranar Asabar ne Oshiomhole ya bayyana haka a taron manema labarai da ya kira a Abuja, ya kuma ce tuni ya umarci lauyoyinsa su janye karar da ya kai na kalubalantar tsige shi a gaban kotun koli.

Tsohon Shugaban Jamiyyar kuma tsohon Gwmanan Edo, yana kalubalantar dakatar da shi ne da aka yi bayan da kotun daukaka kara da jaddada hukuncin dakatar da shi da aka yi tun da farko.

A ranar Alhamis ne aka rusa kwamitin gudanarwa jam’iyyar bayan da kwammitin zartarwa jam’iyyar karkashin jagorancin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta tattauna kan batun.

Oshiomhole ya ce, ya karbi shawarar rusa kwamitin gudunarwa da zuciya daya kuma bashi da wata nadama na kasancewa sa shugaban jam’iyyar.

“A karkashin jagorancina jami’yyyar APC ta samu sakamako mai kyau, amma gahsi an rusa mu to na dauki wannna rusawar da zuciya daya,” inji shi.

“Bazan dauki matakin shari’ar ba kan ko rusa mu ya yi daidai ko bai yi ba, abin lura anan shi ne, shugaban kasa ne ya gayyace ni don na jagoranci jam’iyyar kuma shi ne ya jagoranci zaman tattaunwar da aka rusa mu.

“Shugaban kasa, ne ya gayyace ni don jagorancin jam’iyyar tare da farfado da ita a shekarar 2018, shekara biuy kenan, ya kuma ce mani in har bamu sake fasalin jam’iyyar ba to kawai mu manta da jam’iyyar don za ta mutu.

“Ina mai farinciki cewa, harkar ta zo karshe, an yi zabe a shekarar 2019, muna kuma godiya ga ‘yan Nijeriya, don shugaban kasa ya sam kuri’ar dab a a samu ba a shekarar 2019, muna da sanatoci da majalisar wakilai fiye da da.”

“Ina kima murnar kasancewa an samu zaman lafiya da fahintar juna a stakani majalisar tarayya da kuma bangaren shugaban kasa.” inji shi.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: