Daga Suleiman Ibrahim
Akalla gidaje uku ne aka bada labarin konewarsu a yau Lahadi a wani rikicin kabilanci tsakanin al’umman Omor da Anaku a karamar hukumar Ayamelum ta jihar Anambra.
Kimanin mutane tara, ciki har da wani tsohon Alkalin Alkalan jihar sun samu raunuka daban daban inda aka ce mutum biyu na cikin mawuyacin hali yayin da gidan tsohon Kwamishinan Sufuri yana daga cikin wadanda suka kone kurmus.
Wani mazaunin garin Omor, wanda ya shaida wa jaridar The Nation, ya ce, “Wasu matasa daga al’ummar Anaku sun kai hari ga tsohon Babban Alkali dake garin Omor kuma har sun ji masa rauni a jiki.
“Wasu matasa daga cikin mutanen mu, cikin fushi, suka afkawa garin na Anaku suka kona gine-gine, ciki har da na tsohon Kwamishina da marigayi Sarkin gargajiya na yankin.”
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, mai magana da yawun ‘yan sanda, Tochukwu Ikenga ya ce al’amura sun koma yadda suke cikin lumana tsakanin kabilu Biyun biyo bayan ziyarar da kwamishina Christopher Owolabi da wata tawagar jami’ai suka kai a safiyar yau Lahadi.