Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
ADVERTISEMENT
Home RAHOTANNI

Rikicin Kaduna: Gwamnati Na Neman Yakubu Amos Ruwa A Jallo

by Tayo Adelaja
September 21, 2017
in RAHOTANNI
2 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Musa Muhammad, Abuja

A halin da ake ciki, jami’an tsaro, tare da hadin gwiwar gwamnatin jihar Kaduna sun sanya tsabar kudi har Naira Dubu Dari (N100,000) ga duk wanda ya nuna, ko ya bayyana inda za a kama wani mai suna Yakubu Amos, wanda jami’an tsaron suka zarga da hannu a rikicin da ya auku a kwanakin baya a garin Damisa da cikin Karamar Hukumar Chikun.

Mai ba Gwamnan jihar Kaduna shawara kan harkokin yada labarai, Samuel Aruwan ne ya bayyana haka a wata sanarwar da ya sanya wa hannu jiya Laraba, inda ya ce an cimma wannan matsaya ce a karshen babban taron tsaro na jihar, wanda Gwamna Malam Nasiri Ahmad El-rufai ya jagoranta.

Aruwa ya ci gaba da bayyana cewa Kwamishinan ’yan sanda na jihar, Agyole Abeh ne ya bayyana wa taron cewa rundunar tasa ta yi duk abin da za ta yi don kamo wanda ake nema, amma abin ya ci tura, “don haka ba tare da wata gardama ba, taron ya amince a nemi Amos ruwa a jallo,” in ji Kakakin Gwamnan.

Haka kuma sanarwar ta Aruwa ta bayyana cewa babban taron na samar da tsaro a jihar ya kara jaddada dokar nan da gwamnatin jihar ta sanya na haramta duk wani nau’i na zanga-zanga a kan titunan jihar. “Taron ya kara jaddada wannan doka ce don kare rayuka da dukiyar jama’a,” in ji shi.

Daga nan ya bayyana cewa an ja kunnen duk wata kungiya ko daidaikun jama’a da su yi biyayya ga wannan doka, wanda ya ce gwamnati za ta hukunta duk wani mai kunnen kashi a kan wannann doka, “Muna so jama’a su sani, an sanya wannan doka ne ba don komai ba sai don tabbatar da bin doka da oda, kuma duk wanda ya karya ta zai hadu da hukuncin da ya dace da shi,” in ji sanarwar ta Aruwan.

Cikin wadanda suka halarci wanann zama na jiya, sun hada da Kwamdan rundunar sojoji ta daya da ke Kaduna, Birgediya Janar  GU Chibuisi, Kwamishinan ’yan sanda na jihar Kaduna, Agyole Abeh, Daraktan Hukumar tsaro ta DSS, MT Wakil, Kwamandan sojojin sama na Kaduna,  Air Cdre IT Ali, Kwamandan Kwalejin sojojin ruwa da ke Kachia, Cdre IJ Iliya, Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris, Sarkin Birnin Gwari, Alhaji Zubair Jibril, Mai rike da sarautar Kpop Gwong, Paul Zakka Wyom da sauran shugabannin Hukumomin tsaro da ke jihar.

SendShareTweetShare
Previous Post

Rikicin Kaduna: Gwamnati Na Neman Yakubu Amos Ruwa A Jallo

Next Post

Za Mu Fara Hakar Mai A Sakkwato -Kamfanin NNPC

RelatedPosts

Kasuwa

An Yi Kira Ga ‘Yan Kasuwa Su Rangwanta Wa Al’umma A Watan A Zumin Ramadan

by Muhammad
10 hours ago
0

Daga Alhussain Suleiman, Yayin da al’ummar musulmin Duniya suka fara...

Dalibai

Garkuwa Da Ake Yi Da Dalibai Yaki Ake Da Yankin Arewacin Kasar Nan, Inji Gambo Danpas

by Muhammad
10 hours ago
0

Daga Alhussain Suleiman, Garkuwa da ake yi da daliban a...

Kiwon Lafiya

Shugaban Makarantar Fasahar Kiwon Lafiya Na Kano Yana Ayyukan Da Ke Kare Kimar Gwamna Ganduje–Dokta Amina Ganduje.

by Muhammad
10 hours ago
0

Daga Ibrahim Muhammad, A irin ayyukan jinkai da mutane suke...

Next Post

Za Mu Fara Hakar Mai A Sakkwato -Kamfanin NNPC

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version