Rikicin Makiyaya: An Shata Daga Tsakanin Gwamnan Jihar Binuwe Da Miyetti Allah

Daga Mu’azu Hardawa, Bauchi

Kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore a Nijeriya ta gargadi jama’a da su nisanci sayen shanun Fulani wadanda gwamnatin Jihar Benuwai ta kama da nufin sun keta dokar hana kiwo a Jihar, lamarin da su ka kira a matsayin kwace da kuma nuna fin karfi da gwamnatin ke yi wa Fulani wajen amshe mu su dukiya a lokacin da suka fita domin nemawa dabbobin su abinci kamar yadda suka saba a ko’ina.

Sakataren riko na kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore na kasa, Alhaji Aliyu Abubakar, shi ne ya bayyana haka cikin wata takarda mai shafi guda da kungiyar ta rabawa manema labarai a Bauchi,  inda ta bayyana cewa ba su gamsu da irin matakin da gwamnatin Jihar ta Benuwai ke dauka na kama dabbobin Fulani da ikirarin sun karya dokar hana kiwo ba.

Don haka ya bayyana cewa babu yadda Bafillatani zai ajiye dabba ba tare da ya kai ta daji don cin abinci da kuma kai ta wurin shan ruwa ba, saboda babu wani shiri da aka yi don samar mu su da wurin kiwo na musamman kamar yadda ake yi a ko ina a duniya kafin kafa wannan doka.

Ya ce, karkashin wannan doka da gwamnatin Benuwai da Taraba su ka kafa ta jawo tashin hankali ga Fulani da sauran kabilu inda ake ci gaba da rasa rayuka da dukiya kuma ake dora musu laifi alhali kowa ya san Fulani daruruwan shekaru suke kiwo a kasar nan ba tare da samun matsala ba sai wannan lokacin da wasu kalilan kabilu da suke gadarar sun samu dama ta mulki suka fito da irin wadannan dokoki da nufin cutar da filani ta hanyar nuna kabilanci da banbancin addini da amshe musu dukiya.

Saboda haka Alhaji Aliyu Abubakar ya bayyana cewa ganin wadannan gwamnatoci su na amfani da karfin mulki ta hanyar samar da mutane ’yan kabilar su ana basu makamai don su yaki Fulani su kwashe musu dabbobi hakan ya sa sun kwacewa mutane da dama dabbobi. Saboda ganin ba za su ja da gwamnati ba, amma sun koma ga Allah suna  ci gaba da kai kukan su ga ubangiji domin babu wanda ya isa ya hana su yin hakan saboda zalunci da fin karfi da ake nunawa Fulani akan dukiyar su.

A saboda haka suke jan hankalin mutane da su lura da lafiyar su da mutunci su wajen ganin basu sayi dabba guda ta bafillace da gwamnati ta bayyana cewa za ta yi gwanjon su ba. Don haka ya ce ba za su ja da gwamnati ba, amma duk wanda ya sayi dukiyar su da aka karba bisa zalunci suna ci gaba da hada shi da Allah don haka sun san Allah zai bi kadin su komai na iya faruwa ga wanda ya sayi dukiyar su da aka zalunce su.

Domin kawo karshen rigingimun da ke faruwa kan wannan batu Alhaji Aliyu Abubakar ya roki gwamnatin tarayya musamman shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya yi amfani da kujerar sa ya soke dukkan dokokin da jihohin Taraba da Benuwai suka yi game da hana kiwo, ko kuma ya sa su da kan su su soke dokokin ko su yi gyara na gaskiya wanda ba za a cutar da Fulani ba. Bayan haka kuma  a sa wani kwamiti ko hukuma ta musamman wajen ganin an tabbatar da ikirarin gwamnatin tarayya na duba dokoki da tsarin filayen kiwo da ake da su a kasar nan domin dawo da wuraren da aka sayar wa wasu mutane suka mayar da su gidaje da sauran wuraren amfanin su don a samu zaman lafiya.

Ya kara da cewa hatta kasashen da suka ci gaba basa sanya doka sai sun samar da mafita ta hanyar killace filayen kiwo domin yin ma’ajiyar dabbobi irin ta zamani kafin ace an hana dabbobi yawo domin neman abinci. Amma akwai kuskure game da yadda gwamnati ke ikirarin ta hana kiwo ba tare da wani tanadi na wurin kiwon dabbobi ga Fulani ba alhali duk filayen su mutane masu son zuciya suka warwashe, bayan haka kuma wadannan jihohi ke ikirarin ko bafillace na son barin wadannan jihohi sai ko ya kwashi dabbobin sa a motoci ya fita da su kamar yadda kowa ya ji a kafafen watsa labarai game da wadannan dokoki.

Sakatare Aliyu Abubakar ya bayyana cewa wannan kwamitin riko na kungiya a karkashin jagorancin Alhaji Salisu S. Mohammed  ya himmatu wajen ganin an yi duk abin da za a iya don kare dukiya da martabar Fulani a Nijeriya, don haka su ke jan hankalin gwamnatin tarayya da ta shigo cikin wannan batu da karfin doka don ladabtar da gwamnatocin Benuwei da Taraba wadanda suka fara takalo wutar wannan fitina tsakanin filani da manoma wacce ta ci rayuka da dukiyoyin kowane sashe kuma ta raba mutane da muhallansu. Don haka wannan kungiya a karkashin kwamitin rikon kwarya na kasa take  bukatar gwamnatin tarayya ta dauki matakin soke dokokin nan take domin kowa ya samu kwanciyar hankali a inda yake.

Don haka ya bukaci Fulani a duk inda suke da su himmatu wajen addu’ar Allah ya magance musu wannan matsala ya hukunta duk wani mai son tauye musu rayuwa, Allah ya taimaki wannan gwamnati ta Muhammadu Buhari ta fahimci dukkan masu kawo mata zagon kasa da magance su cikin gaggawa.

Don haka sun gargadi kowane bafulatani ya zauna lafiya da kowace kabila ya kuma nisanci daukar doka a hannunsa ko da wani ya bukaci cin zarafin sa ya kai zuwa ga hukuma don a dauka masa mataki. Yayin da su kuma jami’an tsaro ya bukaci gwamnatin tarayya ta sa ido a kan su don ganin an daina cutar da Fulani a duk inda suke a fadin kasar nan don a samu wanzuwar zaman lafiya a Nijeriya.

 

Exit mobile version