Daga Abubakar Abba
Wasu masana a fanni aikin noma sun yi nuni da cewa, akwai matukar bukatar a yi koyi da Dabarun Gwamnan jihar Kano Dakta Abudullahi Umar Ganduje domin magance rikici a tsakanin Fulani Makiya da Manoma a kasar nan.
daya daga cikin masanan kuma Shugaban yankin Igana Olayiwola Adeleke ya nuna gamsuwar sa kan salon fa gwamnatin Ganguje ta Yi amfani dashi wajen rage rikici a tsakanin Fulani Makiya da Manoma a jihar Kano.
Don a kawo karshen mastalar, masanan sun yi kira da samar da ingantattun dabarun tsaro da kuma ci gaba da sa ido domin a magance matsalar baki daya a kasar.
An dai ta faman yin kira ga mahikuntan dake a kasar nan, kan a tabbatar da an kama dukkan Fulani Makiya da suka yi kutse a gonakan manoman dake kasar nan domin a hukunta su kamar yadda doka ta tanadar.
Masanan sun kuma danganta kan yadda iyakokin kasar nan suke a sakakai ne ke janyo Fulani Makiya bakin haure ke shigo wa cikin kasar nan domin yin kiwo.
Misali, a cewar masanan, a yankin Kudu maso gabas, an kafa dokokin da suka haramta wa Fulani Makiya yin kiwo a gurare barkatai, musamman a tsakanin ‘ya’yan Fulani Makiya yara da sauransu, musamman bayan aukuwar tashin tashina a yankin Igangan da kuma a Sasa dake a cikin jihar Oyo.
Har ila yau, gwamnonin Areeacin kasar nan, sun fito da shirin yin kiwo na Ruga, kamar irin wanda Gwamman jihar Kano Dakta Ganduje ya gudanar a jihar.
A dukkan wadannan jihohin na Areeacin Nijeriya, anja kunnen Fulanin Makiyaya da su su tabbatar sun gudanar da ayyukansu na yin kiwo bisa yadda dokokin jihohin suka gindaya..
Bugu da kari, Nijeriya na iya yin kiwo da tsarin kiwo irin na kasar Tanzaniya inda gwamnatin kasar ke ci gaba da yin kokari wajen dakile rikici a tsakanin Fulani Miakiyaya da Manoman kasar ta hanyar samar da guraren yin kiwo ga Fulani Makiyaya.
Har ila yau, Gwamnan na jihar Kano Abdullahi Ganduje, ya shelanta cewa, gwamnatinsa ta yi namijin kokari wajen rage barayin Shanu, inda ta wanzar da shirin Ruga a jihar.
A cewar Gwamnan na jihar Kano a yankin Samsosua dake da iyaka da Jihar Katsina, kuma mun ci nasara wajen rage ayyukan barayin shanu a yankin.
Gwamnan na jihar Kano Abdullahi Ganduje ya ci gaba da cewa, “ Za mu kuma samar da wasu guraren domin gighina Dam-Dam da Fulani makiyaya za su dinga shayar da dabbobin su”.
A cewar Gwamnan na jihar Kano Abdullahi Ganduje, “Mun kuma kafa asibitin kula da lafiyar dabbobi inda tuni, muka fara gina gidajen Fulani Makiyaya ”.
A cewar Gwamnan na jihar Kano Abdullahi Ganduje ya zama wajibi a kirkiro da dokokin yin kiwo domin a dakile matsalar, inda ya yi nuni da cewa, in kuma ba a yi hakan ba, za a cikin gaba kasa kawo karshen matsalar a kasar nan.
Shi ma mataimakin Gwamnan jihar Biniwe Benson Abounu ya yi nuni da cewa, akwai bukatar a kwaikwayi dabarun Ganduje na kafa Ruga, musamman domin a rage rikicin dake aukuwar a tsakanin Fulani Miakiyaya da Manoman kasar nan.
Ganduje, wanda ya kasance a baya, Makiyayi ne, ya na sane da mafita da ya kamata a dauka domin a kawo karshen matsalar.
A cewar bayanan da kungiyar kasa da kasa ta cording dak bibiyar rikice-rikice a tsakanin alumma (ICG), ta sanar da cewa, yawan rikici a tsakanin Fulani Makiyaya da alumomi ya rubanya hare-haren da ‘yan ta’addar Boko Haram har sau shida domin rikicin na Fulani Makiyaya na aukuwa ne kai tsaye, a tsanakin alumma, inda hakan, ya fi shafar farar hula.
Daga shekarar 2010 zuwa shekarar 2015, an samu rikicin Fulani da Makiyaya guda 850 a yankin Middle Belt, inda kuma aka samu mace-macen mutane guda 6,500 aka kuma raba mutane guda 62,000 daga muhallansu.
A shekarar 2016 kadai, ICG ta tattaro bayanai na mace-macen da ya kai 2,500 a tsakanin Fulani Miakiyaya da Manoma, inda wadanda abin ya fi shafa, sun fito ne daga Jihohin Binuwe da Kaduna sai kuma sauran, daga kudancin kasar nan.