Connect with us

LABARAI

Rikicin Manoma Da Makiyaya: Ka Da Ku Zake Da Kawaicin Da Shugabannin Musulman Nijeriya Ke Maku – Jama’atu

Published

on

Shalkwatar kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) ta yi kira ga gwamnan Jihar Benuwe, Samuel Ortom, da mazugansa da ka da su zake bisa kawaicin da Shugabannin Musulman Nijeriya ke masu kan abin takaici na tashin-tashinan da ke aukuwa da sunan wai ana rikici ne a tsakanin Manoma da Makiyaya.

Wannan yana cikin martanin da Babban Sakataren kungiyar, Shaikh Khalid Aliyu Abubakar , ya sanya wa hannu, wanda martani ne ga wata tattaunawa da wata tashar Talabijin ta yanar gizo ta yi cikin wani shirin ta mai taken, ‘The Osasu Show,’ da gwamnan Jihar ta Benuwe, Samuel Ortom, inda aka ce gwamnan ya bayyana cewa rikicin da ke faruwan na Makiyaya da Manoma a Jihar, “ci gaban Jihadin Shehu Usman Danfodiyo ne.”

Sheikh Abubakar, ya yi gargadi da cewa, sam bai kamata a yi wargi da Shugabannin Musulman wannan kasan ba, musamman a daidai wannan lokacin da ake fuskantar kalubalen tsaro kusan ko’ina a cikin kasarnan, kuma a wannan lokacin na azumin Ramadan, wanda ake umurtan Musulmai da su yi takatsantsan a dukkan lamurransu.

Sashen martanin na cewa, “Domin tarihi ya kiyaye, gwamna Ortom ba shi kadai ne da ke jefa irin wadannan kalaman batuncin ba, Femi Fani Kayode, wanda Minista ne na Jiragen sama zamanin gwamnatin Obasanjo, ya sha yin irin wadannan kalaman batuncin da ba sa faduwa a kan Shehu Usman Danfodiyo.

“Sam Musulunci bai umurci mabiyansa da sukan Addinin wasu ba, ko kuma su rinka jifansu da karya, sai dai ya umurci mabiyan na sa da su kare kansu ne a dukkan lokacin da bukatan hakan ya taso.

“Gwamnan Jihar ta Benuwe ya yi kuskure matuka, kila kuma da gangar ya yi sabili da ya nu na tsananin kiyayyarsa da ta sa yake son keta alfarman shaksiyyar ta Shehu Usman Danfodiyo, wanda Shehu aka san shi da fadin cewa, ‘Gaskiya budadden ciwo ce, wanda adalci ne kadai zai iya yi masa magani.

“Domin fayyace gaskiya ga masu neman kawo rudami, Danfodiyo ya yi Jihadi ne a kan azzaluman Shugabannin Musulmai, inda ya fara da garinsu, da daular Musulmi ta Gobir, ba wai ya fara da yakan wadanda ba Musulmai ne ba. Jihadin na shi ya fitar da al’umma ne daga kangi na zalunci, wanda kuma ya sami karbuwa daga kowa.

“Wannan kuma shi ya sanya dauloli da yawa suka mika wuya a gare shi tun ma kafin a kwama wani yaki. Jihadi ne wanda aka yi shi a bisa turba ta gaskiya da ilimi, kai tun da farko ma sai da Shehu Usmanu ya kirayi Shugabannin da su daina zalunci, kin da shugabannin suka yi na daina zaluntar al’umma ne ya sanya mutane suka taru a wajensa domin yin aikin Jihadin. Shehu Usmanu yana fadin cewa, ‘Al’umma za ta iya zama tare da kafurci, amma ba za ta iya zama a karkashin zalunci ba.”

Daganan sai ya kirayi al’umman Musulmi da ma al’umman kasa bakidaya da su yi watsi da zantukan gwamnan na Jihar ta Benuwe da makamantansa, yana mai cewa, duk zantukan na su karairayi ne kawai ba su da kamshin gaskiya.

Ya kuma yi kira ga Musulmi da su dukufa da addu’o’i musamman a cikin wannan watan mai alfarma na Ramadan domin neman Allah Ya dawo mana da zaman lafiya a kasarmu, a kuma samu yin zaben 2019 lami lafiya, musamman kan yanda ‘yan siyasa ke ta sakin baki da munanan kalamai don neman haddasa rikici.

Advertisement

labarai

%d bloggers like this: