Nasir S Gwangwazo" />

Rikicin Masarauta: Mun Dawo Daga Rakiyar Ganduje, Cewar Dan Gandujiyya

Wani fitaccen dan Gandujiyya a jihar Kano mai suna Kwamred Jamilu Wahada ya bayyana cewa sun dawo daga rakiyar gwamnan jihar, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, a kan rikicin da ya ke yi da Masarautar Kano karkashin jagorancin Mai Martaba Muhammadu Sanusi II ne, saboda yadda rikicin ke dakile ayyukan cigaba da gwamnatin jihar ke gudanarwa.

Kwamred Wahada,  wanda ya yi kaurin suna wajen tallata siyasar Gwamna Ganduje a baya, ya bayyana haka ne a shafinsa na Facebook, ya na mai kira ga sauran ’yan uwansa ’yan Gandujiyya da su kaurace wa shiga wannan rikici, wanda ya ke yin illa ga cigaban jihar.

Idan za a iya tunawa, a kwanakin baya ne gwamnatin jihar ta kekketa Masarautar Kano zuwa gida biyar, inda ta kirkiri masarautu hudu a wani yanayi da a ke kallo na yunkurin rage wa Sarkin Kano ikon fada a ji a fadin jihar.

Haka nan kuma hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar ta dawo da binciken da ta fara yi wa sarkin kan zargin ta’annati da dukiyar masarautar. To, amma masu lura da al’amuran yau da kullum na kallon binciken a matsayin bi-ta-da-kullin siyasa.

Wahada ya ce, tun daga lokacin da a ka fara rikicin, hankalin kowa ya karkata kan rigimar, inda hatta gwamnatin jihar ta bige ta tattalin rigima maimakon mayar da kai ga ayyukan alheri.

Ya ce, “ni Comrade Jamilu Wahada ni dan jam’iyyar APC ne kuma ni dan Gandujiyya ne cikakke (amma) daga yau ku sani cewa, Ina tare da Mai martaba Sarkin Kano Muhamamdu Sanusi II dari bisa dari.”

Ya cigaba da cewa, “Ina kira ga gwamnatin Kano cewa wajibi ne ta taimaki ‘yan jam’iyya wadanda su ka sha wahala a unguwanninsu a lokacin zabe, amma ta ki ta maida hankali a kan rihima da Masarautar Kano, domin a kautar da hankalin ‘yan jam’iyya da mu ka wahala a mazabarmu.”

Exit mobile version