Rikici na kara kazanta a tsakanin bangarorin jam’iyyar adawa ta PDP, yayin da fiye da wakilai 3,000 ke Shirin raba gardama a babban taron jam’iyyar birnin Ibadan na Jihar Oyo, don zabe shugabannin jam’iyyar na kasa.
An tsara taron da za a yi a ranar 15 da 16 ga Nuwamba, 2025, a matsayin wani abu da ke jawo cece-kuce tsakanin bangarorin jam’iyyar guda biyu masu fafutukar neman shugabanci a cikin jam’iyyar.
- Neman Gurbin Kofin Duniya: Nijeriya Ta Lallasa Gabon Da Ci 4
- NDLEA Ta Ƙona Miyagun Ƙwayoyi Sama Da Kilo 52,000 A Kaduna
A daya hannun akwai kwamitin gudanarwar na PDP na kasa karkashin jagorancin shugaban jam’iyyar na kasa, Umar Damagum, wanda ke samun goyon bayan kungiyar gwamnonin PDP da kwamitin amintattu da kuma kungiyar shugabannin jam’iyyar na jihohi da sauran su.
Ko da yake bayan bangaren da Damagum ke jagoranta, akwa kuma bangaren da ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ke jagoranta da ke babbar tasiri, wanda suka zabi shugabansu na kansu, suna kalubalantar gwamnonin a gabansu.
A Juma’a da ta gabata ce, Alkali James Omotosho ya yanke hukunci wanda ya hana shugabancin jam’iyya ci gaba da gudanar da taron da aka shirya. Haka kuma ya hana hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) sa ido a kai, yana mai cewa PDP ta kasa bin ka’idoji, wadanda ke bukatar wasu jami’ai da aka ayyanasu sanar da INEC game da taron.
Bayan hukunci, kwamitin gudanarwa karkashin shugabancin Damagum ta dakatar da sakataren jam’iyyar na kasa, Sanata Samuel Anyanwu da mashawarcin shari’a na kasa, Kamaldeen Ajibade da sakataren shirye-shirye na kasa, Umar Bature na tsawon wata guda saboda zargin ayyukan da ke goyon bayan abin da ya saba wa jam’iyya.
Bayan awanni 24, Anyanwu da magoya bayansa sun hadu a Abuja suka sanar da dakatar da Damagum da dukkan mambobin kwamitin gudanarwa na jam’iyyar.
Sun kuma bayyana sunan mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na Arewa ta tsakiya, Abdulrahman Mohammed, a matsayin sabon mukaddashin shugaban jam’iyya kasa.
Yayin da bangarorin biyu suke kalubalantar junansu, bangaren da Damagum ke jagoranta ya samu umurnin alkalin babban kotun Jihar Oyo, Ladiran Akintola, wanda ya umartar PDP da ta ci gaba da gudanar da taron babban taronta na kasa.
Saboda haka, yayin da Damagum wanda gwamnoni da mambobin kwamitin amintattu da shugabannin jihohi ke goyon baya ke shirin taron, Wike da Anyanwu da wasu sun dage cewa taron ba zai gudana ba.
A sa’ilin da yake magana da ‘yan jarida a ranar Lahadi, wani jami’i a ofishin PDP mai masaniya kan rikicin, ya ce za a taru da wakilai sama da 3,000 a Ibadan don zaben sabbin shugabanni na jam’iyyar.
Ya ce, “Fiye da wakilai 3,000 ne za su raba gardama, kuma ka da ka manta cewa akwai manyan mukamai da za a zaba.
“Lokacin da ka ji mutane waɗdanda abin da suke sha’awa kawai shi ne hallaka jam’iyya suna cewa ba a gudanar da tarukan jam’iyya a wasu jihohi ba, don haka wadannan jihohin ba su da ‘yancin zabe, karya ne dukkaninsu ne saboda har yanzu muna da tsoffin mambobi a wadannan jihohin.”
Wata majiyar wadda take tare da Damagum, ta ce taron zai gudana saboda umarnin Alkali Akintola wanda shi ne mafi girman hukuncin kotu guda biyu da suka bayar.
Ya kara da cewa, “Akwai umarnin kotu guda biyu daga kotunan da ke sauraron shari’ar. A doka, jam’iyya na da ‘yanci ta zabi wanne daga cikin umarnin za ta bi, yayin da wasu lauyoyi ke cewa umarnin karshe (ko na baya-bayan nan) shi ne mafi inganci tun da an bayar da shi daga babban kotun.”
Ya ce bayan an dakatar da Anyanwu daga shugabancin jam’iyya, an ganshi a matsayin mai jagorantar wata kungiya mai batanci, yana kara da cewa, “Duk wanda ke mai da hankali ga kungiyar yana yin hakan ne saboda dalilai na siyasa.
“A bisa tsarin kundin tsarin mulkin PDP, taron kwamitin gudanarwa yana gudana ne bisa umarnin shugaban jam’iyya na kasa, kuma shugaban jam’iyyar na kasa a wannan yanayin shi ne Umar Damagum.
“Dangane da abin da ke sama, daga cikin mambobin kwamitin gudanarwa guda 17 da suka rage, 14 ne suka gana a ranar 1 ga Nuwamba, 2025, suka dakatar da Anyanwu, Bature, Ajibade, da mataimakin mai ba da shawara na kasa a harkokin shari’a, Okechukwu Onuoha.”
Ya yi kira ga kafofin watsa labarai da su daina kiran bangaren da Wike ke jagoranta a matsayin wata bangare na jam’iyyar. Yana bayyana cewa dole ne a gudanar da babban taron jam’iyyar na kasa, kuma dole ne mambobi su fita a filin taron a wuri daya da rana daya, ba abin da Wike da magoya bayansa za su iya yi.
A halin yanzu, Sanata Anyanwu ya ce taron Ibadan ba zai gudana ba. Ya kara da cewa idan wasu shugabannin jam’iyya suka ci gaba da gudanar da shi, INEC ba za ta sa ido a kai ba.












