Connect with us

LABARAI

Rikicin Shugabanci Ta Afka Wa Kungiyar ’Yan Acabar Lokoja

Published

on

Wani sabon rikicin shugabanci ta kunno kai a kungiyar yan acaba ta jihar Kogi, reshen karamar hukumar Lokoja, inda a ka samu baraka tsakanin yan takarar biyu dake neman darewa kujeran shugabancin kungiyar duk da cewa daya bangaren ta zargi shugaban kungiyar ta jiha da neman haddasa rikicin, wanda masu ruwa da tsaki na kungiyar suka yi ga gwamnatin jiha ta karamar hukumar Lokoja dasu tashi haikan wajen shawo kan rikikin kafin lamura sun lalace.

 

Koda ya ke a yayin hada wannan rahotu, gwamnatin jihar ta sanya baki a lamarin inda ta nada wani kwamitin rikon kwarya da zai ja ragamar shugabancin kungiyar ta yan acaba, reshen karamar hukumar Lokoja har sai lokacin da  kunkiyar zata gudanar da sabon zaben shugabanninta, wanda ya kamata a doka a gudanar a ranan 2 ga watan mayun 2020, amma kuma mai baiwa gwamna shawara ta musamman akan sha’anin tsaro a karamar hukumar ta Lokoja, Alh Muhammed Danasabe Muhammed ya nemi a dage zaben saboda dalilan bullar cutar Korona.

 

Rikicin dai ya samo asali ne bayan shugaban kungiyar yan acaban na jihar Kogi wanda har ila yau shine mai rikon kwarya na kungiyar,reshen karamar hukumar Lokoja, Alhaji Gimba K Ibrahim ya mika ragamar shugabancin kunkiyar,reshen Lokoja ga daya daga cikin masu neman takarar kujerar, wato Kwamred Ali Adamu(Police) bayan wa’adinsa na rikon kwarya ta cika a jiya talata.

 

Wakilin LEADERSHIP A YAU wanda ya rika bin lamuran kungiyar tun lokacin data afka cikin rudani ya ruwaito cewa a ranan lara ba ne dai magoya bayan kwamred Baba Aliyu Musa( Baba Guguru) wanda tsohon shugaban kungiyar ne, reshen karamar hukumar Lokoja, kuma a yanzu ya neman sake takarar kujerar,suka yi ta murna bayan sun samu labarin dake cewa an bada umurnin nada gwaninsu a matsayin shugaban kungiyar na rikon kwarya wanda, bincike ya nuna za a rantsar da shi a sakariyar kungiyar dake Lokoja a jiya Amma kuma da sanyin safiyar jiyar sai suka samu labarin cewa tuni shugaban riko na kungiyar mai barin gado,wanda shi ne shugaban kungiyar na jihar Kogi, Alhaji Gimba K Ibrahim yayi gaggawar rantsar da wanda ake zargi dan takarar da yake so ne, wato kwamred Ali Adamu( Police) a matsayin shugaban rikon kwarya na kungiyar yan acaban reshen karamar hukumar Lokoja.

 

Wannan lamari dai ya tada hankulan magoya banyan Kwamred Baba Aliyu Musa da magoya bayansa wanda suke shirin fantsama ofishin kungiyar don rantsar dashi tare da amsar ragamar shugabancin kunkiyar.

 

Wakilin jaridar LEADERSHIP  A yau wanda ya kasance a ofishin kungiyar,ya ga an baza jami’an tsaro dauke da makamai domin dakile barkewar rikici tsakanin magoya bayan yan takarar biyu wadanda suka yi cincirindo a harabar ofishin kungiyar yan acaban dake biirnin Lokoja.

 

Wakilin jaridar LEADERSHIP  A yau ya zanta da manyan yan takarar biyu wadanda ko wannensu ke ikirarin shine jagoran kungiyar yan acaban, reshen karamar hukumar Lokoja.

 

Kwamred Baba Aliyu Musa(Baba Guguru) ya shaidawa wakilimmu cewa shugaban kungiyar mai barin gado, Alhaji Gimba K Ibrahim ne kanwa uwar gamin rikicin kungiyar. Yace akasarin yan acaba suna tare da shi,inda ya kara da cewa tsoron kada dan takarar da yake daurewa gindi ko goyon baya ya fadi zaben,shi yasa yayi maza ya danka masa shugabancin riko na kungiyar, sannan ya bayyana matakin a matsayin haramtacciya wanda ya sabawa doka. Kwamred Baba Musa wanda har ila yau yayi Allah wadai da matakin da shugaban kungiyar mai barin gado ya dauka na nada kwamred Ali Adamu ya kuma yi kira ga dimbin magoya bayansa dasu kwantar da hankulansu tare da yin kira gare su dasu kasance masu bin doka da oda.

 

Har ila yau roki gwamnatin jihar Kogi data shigo al’amarin domin samun zaman lafiya a kungiyar dake neman darewa gida biyu a sabili da son zuciyar wasu masu neman tada zaune tsaye. Daga bisani ya yabawa jami’an tsaro a bisa kokarisu na kaucewa tashin hankali tsakanin magoya bayan yan takara na  kungiyar a sakatariyar kungiyar.

 

A nasa bangaren, kwamred Ali Adamu wanda shima ya zanta da wakilimmu yace ko kadan babu wata baraka a kungiyar. Ya kuma kara  da cewa a yanzu kam,shine shugaban kungiyar na riko da yasha rantsuwa a jiya talata.

 

A don haka ya yi kira ga abokan hamayyarsa dasu hada kai da shi domin ciyar da kungiyar gaba, ya na mai cewa sai da zaman lafiya kungiyar zata cimma burinta.

 

Sai dai kuma labarin da wakilin LEADERSHIP A YAU na nakalto kafin hada wannan rehotu ya nuna cewa kidi ta canza a jiyan, bayan karamar hukumar Lokoja karkashin shugabancin babban mai baiwa gwamna shawara ta musamman akan sha’anin tsaro,Hon Danasabe Muhammed Danasabe  ta sanya baki a batun ganin cewa hakan zai iya haddasa rigima tsakanin magoya bayan yan takarar biyu.

 

A kan haka nema karamar hukumar ta amshe ragamar shugabancin kunkiyar, inda ta rantsar da wani dan kungiyar yan acaban mai suna Kwamred Usman Ibrahim a matsayin shugaba mai rikon kwarya har sai lokacin da aka ware ranan da kungiyar zata gudanar da sabon zaben shugabanninta a dimukradiyance. Karamar hukumar tace ta dauki matakin ne domin raba gardama a tsakanin yan takarar kujerar shugabancin kunkiyar. Kwamred Usman Ibrahim a yayin da yake shan rantsuwar,yayi alkawarin sauke nauyin aka aza masa ba tare da nuna son zuciya ba.

 

Ya kuma sha alwshin tafiya da dukkan yan takarar har lokacin da kungiyar zata gudanar da sabon zaben shugabanninta.

 

A yanzu dai kura ta lafa a tsakanin magoya bayan yan takarar duk da cewa bangaren kwamred Baba Aliyu Musa ba su gamsu da sabon shugaban kungiyar da a ka nada mu su ba, suna mai zargin cewa ba ta canja zani ba.

 

Kokarin da wakilinmu ya yi don zantawa da shugaban kungiyar mai barin gado, Alhaji Gimba Ibrahim, ya ci tura.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: