Wata kotun yanki a Yola fadar jihar Adamawa, ta bada umurnin jami’an tsaron ‘yan sanda da su ci gaba da tsare membobin jam’iyyar PDP (ma su neman sauyi), biyo bayan zargin sun aikata ta’addanci, ‘yan jebu da kuma hana jama’a sakat a gari.
Da ya ke yanke hukuncin ranar Laraba, mai shari’a Dimas Elshama, ya ce ya yanke hukuncin ne bisa tanadin da sashe na 294 ya yi, da ya ke matakin sulhunta ma su karekai uku da mai gabatar da kara, ya ci tura.
Don haka alkalin ya yanke hukuncin cewa jami’an tsaron ‘yan sanda su ci gaba da tsare wadanda ake zargi uku, kamar yadda shugaban bangaren gabatar da kara Director Public Prosecution (DPP), ya bada shawari.
Ya ce toshen hukuncin yana bisa doka, ya ce kokarin bangaren lauyoyin ma su karekai na ganin sun kare mutanen da’ake zargin ba su da hujja, dalilan da su ka bayar ba karbabbu ba ne.
Alkalin kotun ya kuma umurci jami’i mai gabatar da kara da ya tabbatar, shawarin da DPP ya bayar ta samu kafin ranar 20 ga Afrilun 2020.
Da ya ke magana da ‘yan jaridu bayan gabatar da shari’ar shugaban tawagar lauyoyin da ke kare mutanen da’ake zargi Baresta Jerry Owe, ya ce kotun bata da hurumin ci gaba da garkame mutanen bisa la’akari da laifukan da’ake tuhumar wadanda ya ke karewa.
Ya ci gaba da cewa laifukan da’ake tuhumar mutanen da mai gabatar da kara ya gabatar, babu hujjar da ba za’a sauraresu ba, ya ce bayan da aka kyalesu su kafa hujja, ma su karekansu su na da ‘yancin a sauraresu, kuma aji daga garesu.
Barista Owe, ya ce ya lura da cewa cikin sharudan caji ukun da za’a cika daya ne kawai aka cika, sauran biyun kuma basu samu ba, ya ce a wannan kasar kotu bata da irin wannan ‘yancin da za ta ci gaba da irin wannan tsarin.
Ya ce “cikin sharuda ukun, daya ne kawai bayanansa ya gabata ga kotu, na 8 kuma ba’a cike ba, kuma tabbatar da takardar rantsuwa bai yiwu ba” inji Owe.
Da shima ke magana game da hukuncin shugaban r-PDP a jihar Dakta Umar Ardo, ya kalubalanci alkalin kotun da bari ayi amfani dashi, akan abubuwan da ya ce wasa ne irin da ta shafi harkokin siyasar jihar.
Ya ci gaba da cewa gabadaya hukuncin alkalin kotun ya yi hanun riga da umurnin babban alkalin alkalai na qasa, da dama ya dakatar da duk wani zaman kotu zuwa 20 ga Afrilun 2020, saboda matsalar annobar Koronabairus.
Ardo ya ce zai rubuta takardar korafi ga majalisar alkalai ta kasa (NJC), domin kalubalantar abinda ya bayyana da rashin kwarewar gudanar da hukunci.
Ya ce kuma zai rubuta wata takardar korafin ga ofishin shugaban rundunar ‘yan sanda ta kasa, game da yadda kwamishinan ‘yan sandan jihar Audu Madaki, ya bari ana amfani dashi kan harkokin da su ka shafi siyasa a jihar.