Rikicin Taron APC Ya Ci Kujerar Darakta Janar Na Kungiyar Gwamnonin APC

Salihu Lukman

Rikicin cikin gida da ake yi a tsakanin gwamnonin APC da Kwamitin Shugabancin Jam’iyyar a karkashin Gwamna Buni na Yobe game da babban taron jam’iyyar na kasa ya ci kujerar darakta janar na kungiyar gwamnonin jam’iyyar, Salihu Lukman wanda ya yi murabus daga mukaminsa.

Wasu dai na ganin bai kamata darakta janar din ya yi murabus a irin wannan lokacin ba, yayin da wasu kuma ke ce masa “Allah raka taki gona”.

A jiya Lahadi dai gwamnonin APC rankacakaf sun yi taro a Abuja a kan batun taron, inda suka cimma matsayar cewa lallai kar a bari watan Fabarairu ya kare ba tare da an gudanar da taron ba.

 

Exit mobile version