Abba Ibrahim Wada">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home WASANNI

Rikita-Rikitar Da Ta Baibaye Dangantakar Ozil Da Arsenal

by Abba Ibrahim Wada
January 18, 2021
in WASANNI
5 min read
ozil
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Kusan yanzu zamu iya cewa ta faru ta kare domin dan wasa Mesut Ozil ya amince da komawa kungiyar kwallon kafa ta Fenerbahce bayan Arsenal ta amince da ruguza ragowar yarjejeniyar da take tsakaninta da dan wasan dan asalin kasar Jamus.

Zamu iya cewa yanzu dan wasan tsakiyar na Arsenal Mesut Ozil ya kusa kammala kulla yarjejeniyar tafiya kungiyar kwallon kafar Fenerbahce da ke Turkiyya bayan daukar tsawon lokaci ana sa’insa tsakanin dan wasan da Arsenal.

samndaads

Har yanzu akwai sauran rabin kakar wasa guda daya kafin wa’adin kwangilar dan wasan mai shekara 32 ta kare ta Arsenal sai dai dukkan bangarorin sun yi nisa a tattaunawa wadda ake sa ran za ta kai ga gintse kwangilar tasa kuma hakan zai ba shi damar tafiya Istanbul a kwanaki masu zuwa.

Arsenal ba ta sanya Ozil a wasa ba tun wasan da suka doke kungiyar kwallon kafa ta West Ham United da ci 1-0 a watan Maris din shekarar data gabata kuma kociyan kungiyar, Mikel Arteta ya juya masa baya gaba daya.

Ozil ya bayyana shaukinsa na tafiya Fenerbahce a wani shirin tambaya da amsa da ya gudanar a shafukan sada zumunta a wannan makon inda ya shaida wa mabiyansa cewa Fenerbahce kamar yadda Real Madrid da ke Spain take ita ce kungiya mafi girma a kasar.

Rahotannin da wasu kafafen watsa labaran Turkiyya suka bayar a farkon wata sun nuna cewa Fenerbahce za ta dauki Ozil a watan nan na Janairu kuma tuni Magana tayi nisa a wannan satin kuma a wannan satin zai kammala barin Arsenal.

An haifi Ozil a Jamus amma iyayensa ‘yan asalin Turkiyya ne, kuma a baya shugaban Fenerbahce Ali Koc ya ce babban burinsu shi ne su dauki Ozil sannan a shekarar 2019 kungiyar ta Turkiyya wadda sau 19 tana lashe kofin Super Lig ta ce ba za ta dauki Ozil ba saboda ba ta da kudi.

Kungiyar ta fada matsin tattalin arziki a shekarun baya bayan nan lamarin da ya bai wa kungiyar Istanbul Basaksehir damar lashe kofin a karon farko a watan Yulin da ya gabata sai dai ana ganin yanzu kungiyar ta farfado..

Ozil ya buga wasa a wasanni 10 tun bayan da aka nada Arteta a matsayin kociyan Arsenal a watan Disamba na shekarar 2019, sai dai bai sake buga wasa ba tun da aka koma wasanni bayan dokar kullen farko sanadin barkewar annobar korona a watan Yuni.

 

Me Ozil Ke Cewa?

Ozil, wanda tsohon dan wasan tawagar kwallon kafar Jamus ne yana daf da barin kungiyar kwallon kafa ta Arsenal sakamakon maida shi saniyar ware da mai horar da ‘yan wasan kungiyar Mikel Arteta yayi saboda wasu dalilai da har yanzu babu wanda ya sansu.

Dan wasan ya sha nanata cewa yana jin lafiya kamar ingarman doki, kuma a shirye yake ya yi wasa amma Arteta baya amfani dashi wanda hakan yasa aka dinga sukar Arteta a kwanakin baya sakamakon rashin kokarin kungiyar duk da cewa ana ganin idan ya yi amfani da Ozil zai taimaka masa.

Tsohon dan wasan na Werder Bremen ya fito sosai a dandalin sada zumunta tun lokacin da aka daina ganinsa a filin kwallo, inda har a rana Litinin da ta gabata ya dinga amsa tambayoyin masu bibiyansa a Twitter kuma ba tare da nuna wata damuwa ba.

Dan wasan wanda ya lashe kofin duniya da kasar Jamus a shekara ta 2010 ya amsa tambayoyi da dama da suka hada da wadda akayi masa mai cewa ko yana da na sanin zuwa Arsenal sai dai dan wasan ya bayyana cewa bai taba danasanin komawa kungiyar ta Arsenal ba a rayuwarsa.

Sai dai bayan da yanzu aka fayyace makomarsa a Arsenal, Mesut Ozil ya ce baya nadamar kulla yarjejeniya da kungiyar da kawo yanzu ya shafe akalla shekaru 7 tare da ita duk da kalubalen daya fuskanta.

Ozil dai yana daya daga cikin manyan ‘yan wasan duniya wadanda suka shahara wajen sarrafa kwallo da taimkawa a zura kwallo sannan kuma ya kware wajen kwantar da hankalin ‘yan wasa a lokacin da wasa baya yiwa kungiyarsa yadda ta ke so.

Sai dai a baya bayan nan tauraron Ozil ya dusashe a kungiyar ta Arsenal, musamman bayan da Mikel Arteta ya karbi jagorancin horas da kungiyar, wanda ya cire Ozil daga tawagarsa baki daya a kakar wasa ta bana.

Sai dai duk wannan koma baya, Ozil ya ce bai taba yin nadamar kulla yarjejeniya da Arsenal ba duk da cewa cikin wannan wata na Janairu ya kulla yarjejeniya da kungiyar kwallon kafa ta Fanaberche dake kasar Turkiya bayan da kungiyar ta shiga gaba tsakanin kungiyoyin dake neman kulla yarjejeniya da shi.

 

Yadda Aka Samu Rabuwar Kai A Arsenal Akan Ozil:

Akwanakin baya rahotanni  daga kungiyar ta Arsenal sun ce an samu rarrabuwar kai tsakanin ‘yan wasan kungiyar, dangane mayar da dan wasan Mesut Ozil cikin tawagarsu a watan Janairun nan da muke ciki.

Rahotanni sun bayyana cewa wasu daga cikin ‘yan wasan kungiyar suna goyon bayan a mayar da Ozil cikin tawagar domin zai taimakawa kungiyar duba da halin da suka shiga a kwanakin baya na rashin samun nasara wadda kuma aka alakanta hakan da rashin kwararre wajen sarrafa kwallo kamar yadda Ozil din ya keyi.

Sai dai wasu kuma suna ganin shigowar dan wasan a cikin watan Janairu bata da amfani saboda tuni an shirya kakar wasa ta bana babu shi kuma alakar dan wasan da kociyan kungiyar bata da kyau hakan yasa suke ganin idan ma ya dawo buga wasa babu tabbas idan zai samu damar buga wasanni akai-akai sannan kuma zaiyi wahala idan zai iya bawa kungiyar abinda take bukata.

Rikicin Ozil da Arsenal dai ya samo asali ne tun a lokacin tsohon kociyan kungiyar, Unai Emery sannan kuma Arteta shima yazo ya dora duk da dai wasu suna ganin manyan shugabannin kungiyar ne suke da ruwa da tsaki akan rikicin dan wasan da kungiyar.

Ozil dai yanzu y agama duk wani shiri na barin Arsenal, kungiyar daya koma daga Real Madrid  kuma tun zuwansa ya taimakawa kungiyar ta lashe gasar cin kofin kalubake na FA sannan sunje wasan karshe na gasar Europa kafin Chelsea ta doke su a wasan karshe.

SendShareTweetShare
Previous Post

Ya Tsunduma Motarsa Cikin Kogi Yayin Da Yake Bin Umarnin ‘Google Map’

Next Post

An Dage Babban Zaben Shugaban Barcelona

RelatedPosts

PSG

Bambancin Tuchel Da Pochettino A PSG

by Abba Ibrahim Wada
1 day ago
0

Ranar Lahadi kungiyar kwallon kafa ta Monaco ta je har...

Kallo

’Yan Kallo Za Su Koma Shiga Kallo A Watan Mayu A Ingila

by Abba Ibrahim Wada
1 day ago
0

Kimanin 'yan kallon kwallon kafa 10,000 za su koma shiga...

Yadda Aka Raba Jadawalin Kofin Zakarun Afrika

by Abba Ibrahim Wada
1 day ago
0

An hada kungiyoyi uku da suka taba lashe kofin zakarun...

Next Post
Zaben Shugaban Barcelona

An Dage Babban Zaben Shugaban Barcelona

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version