Ritayar Dole: Jami’ai 37 Da Aka Sallama Sun Maka Rundunar Sojin Nijeriya A Kotu

Mazauna Kauye

Wasu sojoji 37 da aka yi wa ritayar tilas da suka hada da janar-janar da kanar-kanar, sun maka Rundunar Sojin Nijeriya a Kotun ECOWAS, inda suka nemi a haramta ritayar dolen da aka yi musu.

Ita ma matar marigayi Laftanar Kanar O.A Baba-Ochankpa na cikin wadanda suka maka rundunar sojin Nijeriya din a kotun. Wadannan manyan jami’an sojoji 37 tare da matar marigayi Baba-Ochankpa, sun shigar da karar ce ta hannun lauyan su mai suna Abdul Muhammed.

Ita matar Ochankpa, ta shiga cikin jerin masu karar a madadin mijin ta da ta ke wa takaba. Jami’an sojojin 37 da aka yi wa ritayar dole, sune Manjo Janar 9, Birgediya Janar 10, Kanar 7, Laftanar Kanar 11 da Manjo 1.

Sun yi ikirarin cewa an ladabtar da su ta hanyar yi musu ritayar dole a ranar 9 Ga Yuni, 2016. Cikin wadanda aka hada tare da rundunar sojan Najeriya aka maka kotu, har da gwamnatin tarayya ita kan ta.

Masu korafin sun bayyana cewa an tauye tare da danne musu ‘yancin su, ta hanyar yin amfani da ejan-ejan din su wato Ministan Tsaro na lokacin, Mansur Dan’Ali; Shugaban Hafsan-hafsoshin Sojoji, Abayomi Olonisakin, da kuma Babban Hafsan Hafsoshin Najeriya, Tukur Buratai.

Sakamakon wannan zargin tauye musu ‘yanci da takurawar da suka shiga su da iyalan su, sun nemi kotu ta tilasta a biya su diyyar naira bilyan 10. Tare da cewa ritayar dolen da aka yi musu haramtacciya ce.

Exit mobile version