Connect with us

KASUWANCI

Robobin Da Ake Watsawa A Cikin Teku Za Su Rubanya Halittun Dake Cikin Teku Nan Da 2050 —MASANA

Published

on

Sashen yada labarai na Majalisar dinkin duniya ta yi gargadin cewar, in har kasashen duniya basu daina watsa robobin da aka yi amfani dasu a cikin tekuna ba, yawan robobin zai rubanya yawan dabbobin dake cuikin tekuna nan da shekara 2050 masu zuwa..
Kididdiga ta nuna cewarmutane da dama suna daga cikin wadanda suke janyo zuba robobi a cikin tekuna.
Fanni daya ba zai zamo musabbabin fadawar sama da tan din robobi 200,000 da suke kwarara zuwa cikin tekuna ba a duk shekara ba Nijeriya.
Har ila yau, majalisar dinkin duniya ta bayyana cewar, a kalla tan miliyan takwas na robobin da aka yi amfani dasu suke kwarara zuwa cikin tekuna duk shekara.
A jawabin sa a taron ranar muhalli ta duniya da aka gudanar a kwanan baya a jahar Legas Dakta Ronald Kayanja, ya koka akan yadda mutane suke zuba robobin da aka yi amfani dasu a cikin tekuna.
A cewar sa, baya ga shafar lafiyar alumma, jefa robobin da aka yi amfani dasu a cikin tekuna suna kuma janyo kalubalen haifar da cutar kansa da kuma sauran cututtuka.
A jawabin sa na maraba a wurin taron, Manajin Darakta na hukumar filayen jiragen sama ta kasa Injiniya Saleh Dunoma yace, bai kamata a danga matsalar akan fanni daya ba musamman ma’aikatar sufuri ba.
Shi kuwa Farfesa Babajide Alo a tashi kasidar da ya gabatar a wurin taron yace, ana sarrafa sababbin robobi biliyan dari uku duk shekara a fadin duniya, inda yace kashi kashi goma bisa dari na robobin suna kwarara ne zuwa cikin tekuna haka kuma kashi saba’in suna da suke kwarara cikin tekunan suna janyowa alumma da kuma dabbobin da cututtuka .
Babajide Alo ya yi kira ga mahukunta dasu samar da doka mai karfi da zata hana watsa robobin da aka yi amfani dasu a cikin teku, inda ya ya yi nuni da cewar, tuni kashashen Kenya da Rwanda suka fara kokarindakile hakan.
Ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya data kara harajin da take karba akan kamfanonin da suke sarrafa robobi don magance hakan.

Advertisement

labarai