Bangladesh ta ce, za ta takaita zirga-zirgar ‘yan gudun hijira na kabilar Rohingya da suke shigo mata, bayan tserewa daga Myanmar.
‘Yan sandan kasar sun ce tilas ne ‘yan gudun hijirar na kabilar Rohingya, su zauna a sansanonin wucin gadin da gwamnati ta basu a maimakon fantsama cikin kasar.
Gwamnatin Bangladesh ta kuma sanar da shirinta na gina manyan sansanoni a birnin Cod’s Bazar da za su ishi ‘yan kabilar ta Rohingya sama da 400,000 da suka tsere daga Mynamar, inda kungiyoyin kare hakkin dan’adam suka zargi sojin kasar da kone gidajen ‘yan kabilar mafi akasarinsu Musulmi, da sunan kokarin murkushe mayakan ARSA.
A karshen makon nan dangantaka ta yi tsami tsakanin kasashen biyu, bayanda Bangladesh ta zargi Mynammar ta keta mata iyaka ba bisa ka’ida ba.