Abba Ibrahim Wada" />

Rohr Ya Jinjina Wa ‘Yan Wasan Super Eagles

Kociyan tawagar ‘yan wasan Super Eagles ta Nigeriya, Gernot Rohr, ya jinjinawa tawagar ‘yan wasansa bayan da suka samu nasara akan tawagar ‘yan wasan kasar Benin duk da cewa tun farko Nigeria aka fara zurawa kwallo a raga.

Dan wasa Stephen Sessegnon ne ya fara zura kwallo a ragar Nigeria minti biyu da fara wasa kafin kuma dan wasan Bictor Osimhen ya farkewa Nigeria sannan kuma Samuel Kalu ya kara kwallo ta biyu a wasan da suka fafata na neman cancantar shiga gasar cin kofin nahiyar Africa.

Sai dai kociyan na Nigeria, ya bayyana irin farin cikinsa da nasarar da ‘yan wasan nasa suka samu inda yace ‘yan wasan sun burgeshi duba da yadda suka dage sosai suka farke kwallon da aka zura musu tun fakon wasan.

“’Yan wasan kasar Benin suna da kwarewa sosai saboda kowa yasan irin wasan da suka buga a gasar cin kofin nahiyar Africa wadda aka buga a kasar Masar saboda haka buga wasa dasu akwai wahala sosai ga duk wanda yasansu” in ji Rohr

Ya cigaba da cewa “Ina farin ciki da nasarar da muka samu domin hakan shine yake nuna cewa ‘yan wasana sun shirya sadaukar da komai ga wannan tawaga tamu kuma munyi farin ciki da karbar da magoya baya suka bamu”

Nasarar da Super Eagles din ta samu yasa kawo yanzu tana matsayi na farko akan teburin nasu bayan da kasashen Lesotho da Sierra Leone suka tashi 1-1 a wasan da suka buga kuma yanzu a ranar Lahadi Nigeriya zata kai ziyara kasar Losotho domin buga wasan karshe.

Exit mobile version