Connect with us

WASANNI

Roma Ta Shirya Sayar Da Under Cengis

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Roma da ke kasar Italiya ta shirya sayar da dan wasanta na gaba, Under Cengiz, wanda kungiyoyi da dama a nahiyar turai suke bibiya saboda yadda matashin dan wasan ya ke buga a wasa mai kyau tun yana da kana nan shekaru.

Kungiyoyin Manchester United da Arsenal ne dai suke zawarcin dan wasan gaban, Cengiz Under, wanda kungiyarsa tayi masa farashin fam miliyan 27 ga duk kungiyar da take fatan sayansa a kakar wasa mai zuwa.

Matashin dan wasan dan asalin kasar Turkiyya yaja hankalin manyan kungiyoyin ne bayan ya zura kwallaye 19 sannan ya taimaka an zura guda 12 cikin wasanni 85 din daya bugawa kungiyar a zaman da yayi a birnin na Roma da ke kasar Italiya.

Tuni Manchetser United da Arsenal suka nuna sha’warsu ta sayan dan wasan gaban wanda suke ganin ba zaiyi tsada ba sosai sannan kuma matashin dan wasa ne wanda nan gaba idan ya goge zai iya zama shahararren dan wasan duniya.

Sakamakon annobar cutar Korona tasa kungiyoyi da dama ba zasu iya kashe kudade da yawa ba a kasuwar saye da sayar da ‘yan wasa ta bana hakan yasa ake ganin abune mai wahala Manchester United ta iya biyan fam mliyan 100 wajen sayan Jardon Sancho na kungiyar Dortmund wanda United din ta dade tana zawarci.

kungiyar kwallon kafa ta Roma tana fatan sayar da dan wasan domin samun kudin da itama zata kashe a kasuwar saye da sayar da ‘yan wasa ta bana kuma tuni ta shirya fara tattaunawa da duk kungiyar da zara iya biyan farashin da tayiwa dan wasan.

Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Mikel Arteta, ya bayyana cewa kungiyar zata shiga kasuwar saye da sayar da ‘yan wasa domin sayan ‘yan wasan da suka dace da kungiyar kuma ya tabbatar da cewa shugabannin kungiyar a shirye suke dasu bashi goyon baya ta hanyar bashi kudi domin sayan ‘yan wasan da ya keso

dan wasa Under Cengiz dai yasha fama da ciwo a wannan kakar sai dai kungiyar Roma ta yanke shawarar sayar da shi idan har an samu kungiyar da za ta biya abinda take bukata akan dan wasan nata wanda a kwanakin baya Barcelona ma tayi zawarcinsa
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: