Roma Ta Yi Allah Wadai Da Harin Da Magoya Bayanta Suka Kai Wa Na Liverpool

Kuniyar kwallon kafa ta AS.Roma ta yi Allah wadai da harin da wasu tsirarun magoya bayanta suka kai wa magoya bayan Liverpool a kusa da filin wasa na Anfield awanni kadan kafin wasan da kungiyoyin suka buga a Ranar Talata.

Wani fefen bidiyo da aka dauka ya nuna yadda wasu magoya bayan kungiyar Roma suka kai wa na Liverpool hari lokacin da suke zaune suke jiran shiga filin wasan inda aka jiwa wani magoyin bayan Liverpool mai shekara 53 ciwo a kansa.

Roma dai ta nuna rashin jindadinta ga lamarin kuma ta yi Allah wadai da harin sannan kuma ta bayyana kudirinta na hada kai da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool da hukumar kwallon kafa ta nahiyar turai da jami’an tsaro domin hukunta wadanda ake tuhuma da laifin.

A sakon da kungiyar ta fitar, ta kuma mika sakon jajenta ga magoyin bayan da aka jiwa ciwon da iyalansa sannan kuma ta yi masa fatan warkewa cikin gaggawa.

A karshe kungiyar tace wannan halin da wasu magoya bayanta suka nuna abin kunya ne suka jawowa kungiyar a idon duniya kuma sunyi Allah wadai dashi sannan kuma zasu dauki mataki na gaba domin ganin hakan bata sake faruwa ba.

Tuni dai jami’an tsaro suka cafke wasu mutane biyu da ake zargi yan birnin Rome ne na kasar Italiya wadanda ake zargin sunada hannu aciki.

 

Exit mobile version