Abba Ibrahim Wada" />

Ronaldo Na Son Karin Albashi A Real Madrid

Dan wasa Cristiano Ronald ya nemi kungiyarsa ta Real Madrid ta kara masa albashin da yake karba zuwa Euro 500,000 a mako daya kamar yadda yake a tsarin bayar da albashi.

Ronaldo ya nemi karin ne bisa sharadin idan har ya taimakawa kungiyar lashe kafin gasar zakarun turai karo na uku a jere, za a tabbatar masa da karin albashin.

Dan wasan dai yana neman yin kafada da kafada ne da abokin hamayyarsa Lionel Messi, wanda a yanzu shi ne yafi kowane dan kwallon kafa yawan albashi.

Rahotanni sun bayyana cewa watakila bukatar ta Ronaldo ta haddasa rarrabuwar kai a tsakanin ‘yan wasan Real Madrid domin akwai yiwuwar ya sake yin barazanar barin kungiyar muddin aka ki sauraron bukatarsa.

Yan wasa irinsu Casemiro da Carbajal da Asensio dai sun nuna bukatar su ta karin albashi a kungiyar kuma kungiyar tace a kakar wasa mai zuwa zata kara musu albashin.

’Yan wasa irinsu Gareth Bale da Karim Benzema duk suna karbar albashi mai tsoka a kungiyar sai dai watakila kungiyar zata rabu dasu domin samun rarar kudin karawa wasu yan wasan albashi.

Exit mobile version