Ronaldo Ya Fara Tunanin Qungiyar Da Zai Koma

Ronaldo

Dan wasa Cristiano Ronaldo yana nazari a kan kungiyoyin da suke bukatar ya buga musu wasa a kakar wasa mai zuwa biyo bayan jita-jitar cewa akwai yiwuwar zai bar kungiyar kwallon kafa ta Jubentus a wannan bazarar.

Wakillin dan wasan mai shekaru 36 su na duba bukatun da kungiyoyi da dama suka mika na dan wasan, kuma cikin kungiyoyin da ke neman sa har da kungiyar kwallon kafa ta Paris St Germain da tsofaffinkungiyoyinsa Real Madrid da Manchester United.

Masu tafiyar da harkokin na Ronaldo ba za su yanke shawara a game da makomar dan wasan ba har sai bayan gasar cin kofin nahiyar Turai ta Euro 2020, amma sun ce lallai akwai yiwuwar canza sheka za ta yi wuya, saboda albashin da za a rika biyansa da kuma farashin da Jubentus ta sanya a kansa sun yi yawa.

Ronaldo ya riga ya tattauna da sabon kocin Jubentus Massimiliano Allegri bayan da ya maye gurbin Andrea Pirlo  a matsayin mai horas da kungiyar da ke Turin na kasar Italia, kuma an shirya karin tattaunawa kafin kungiyar Serie A din ta fara atisayen tarbar kaka mai zuwa

Exit mobile version