Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Juventus, Cristiano Ronaldo ya kafa sabon tarihin cin kwallaye ranar Lahadi, inda ya zama dan wasa na farko da ya ci kwallo 15 a kakar wasanni 15 da ta wuce a Ingila da Spain da kuma Italiya.
Kyaftin din na Portugal ya ci kwallo a karawar da Jubentus ta doke kungiyar Sassuola 3-1 a gasar Serie A da suka fafata ranar Lahadi wasan da Jubentus din tasha wahala kafin a tashi daga fafatawar.
Ronaldo ya ci kwallaye 15 a kakar wasa ta bana a wasanni 13 da ya buga, kuma kwazon da yake sawa a kowacce shekara kenan tun daga shekarar 2006 zuwa 2007 a lokacin da ya buga wasa a kungiyar kwallon kafa ta Manchester United da Real Madrid da kuma Jubentus.
Dan wasan ya koma Jubentus ne a shekarar 2018 daga Real Madrid ya kuma lashe kofin Serie A biyu a jere, ya ci kwallo 84 a wasanni 104 da ya yi wa kungiyar kuma kawo yanzu Ronaldo ya ci wa kungiya da tawagar Portugal kwallaye 759 jumullah idan aka hade.