Ronaldo Ya Sake Kafa Tarihin Cin Kwallaye

Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Juventus, Cristiano Ronaldo ya kafa sabon tarihin cin kwallaye ranar Lahadi, inda ya zama dan wasa na farko da ya ci kwallo 15 a kakar wasanni 15 da ta wuce a Ingila da Spain da kuma Italiya.

Kyaftin din na Portugal ya ci kwallo a karawar da Jubentus ta doke kungiyar Sassuola 3-1 a gasar Serie A da suka fafata ranar Lahadi wasan da Jubentus din tasha wahala kafin a tashi daga fafatawar.

Ronaldo ya ci kwallaye 15 a kakar wasa ta bana a wasanni 13 da ya buga, kuma kwazon da yake sawa a kowacce shekara kenan tun daga shekarar 2006 zuwa 2007 a lokacin da ya buga wasa a kungiyar kwallon kafa ta  Manchester United da Real Madrid da kuma Jubentus.

Dan wasan ya koma Jubentus ne a shekarar 2018 daga Real Madrid ya kuma lashe kofin Serie A biyu a jere, ya ci kwallo 84 a wasanni 104 da ya yi wa kungiyar kuma kawo yanzu Ronaldo ya ci wa kungiya da tawagar Portugal kwallaye 759 jumullah idan aka hade.

Dan wasan shi ne a kan gaba a ci wa Real Madrid kwallaye a tarihin kungiyar domin yana da kwallaye 450 a raga, kuma shi ne gaba a tawagar Portugal da kwallaye 102, kuma shi ne dai kan gaba a zazzaga kwallaye a raga a gasar cin kofin zakarun turai na Champions League inda yaci kwallaye 134.

Exit mobile version