Ronaldo Ya Warke Kuma Ya Shiryawa Liberpool – Zidane

 

Mai koyar da yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid Zinadine Zidane, ya ce Cristiano Ronaldo ya shirya tsaf don tunkarar wasan karshe na lashe kofin zakarun Turai da zai gudana ranar Asabar 26 ga watan nan, wato nan da kwanaki 6 masu zuwa.

Zidane ya kuma tabbatar da cewa Ronaldon zai buga wasan sada zumunta da karamar kungiyar zata buga a ranar Litinin, dan wasan da a baya ake rade-radin ba zai buga ba kasancewar yana shiryawa wasan karshe na lashe kofin zakarun Tura.

A wasu lokutan Zidane din kan ajje Ronaldon a benci musamman idan yasan akwai wani wasan da yafi wannan muhimmanci a gaba, kamar dai salon da ya yi amfani da shi wasanninsu da Malaga, Las Palmas da kuma Espanyol duk dai a gasar La Liga la’akari da yadda suka zo gab da wasu wasanni na cin kofin zakarun Turai, matakin kenan da ake ganin ya haddasa musu koma baya a gasar ta La Liga.

Ronaldon dai yanzu haka ya na fama da gurdewa a kwaurinsa sakamakon raunin da ya samu yayin faftawarsu da Barcelona matakin da wasu ke ganin ba lallai ya iya abin kirki a wasansu da Liberpool ba.

 

Exit mobile version