Ronaldo Ya Yi Magana Kan Ritayarsa Daga Kwallo

Cristiano Ronaldo ya bayyana cewa ba shi da niyyar yin murabus daga harkar kwallon kafa a yanzu, bayan ya taimaka wa tawagar kasarsa ta Portugal lashe kofin gasar ‘Nations League’ na manyan tawagogin kasashen Turai na farko a ranar Lahadi.

Ronaldo dan shekara 34 bai taka rawar gani a wasan karshe mara armashi da ya gudana tsakanin Porutgal da Netherlands a garin Porto ba, wasan da Portugal ta doke Netherlands da ci daya mai ban haushi, kwallon da Goncalo Guede ya ci.

Amma bayan ya dan jingine murza wa kasarsa tamaula har aka gama matakin rukuni na gasar, Ronaldo ya dawo ya taka gagarumar rawa wajen kai kasarsa wasan karshe na gasar, bayan ya ci kwallaye uku rigis a wasan kusa da na karshe da Portugal ta doke Switzerland.

Duk da ‘yan wasa matasa masu hazaka a tawagar Portugal kamar su Bernado Silva na Manchester City, Ronaldo yana da niyyar ci gaba da taka leda a tawagar har zuwa lokacin da za ta kare kanbunta a shekara mai zuwa.

Wannan nasarar da Portugal ta samu a ranar Lahadi ta yi wa Ronaldo dadi kasancewar shi ne dan wasa daya tilo da ya rage cikin ‘yan wasan tawagar kasar da ta sha kashi a hannun Greece a wasan karshe na gasar cin kofin nahiyar Turai a 2004.

Ronaldo dan shekara 34 bai taka rawar gani a wasan karshe mara armashi da ya gudana tsakanin Porutgal da Netherlands a garin Porto ba, wasan da Portugal ta doke Netherlands da ci daya mai ban haushi, kwallon da Goncalo Guede ya ci.

Exit mobile version