Ronaldo Ya Zura Kwallo Ta 800 A Rayuwarsa

Ronaldo

Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United,Cristiano Ronaldo ya ci kwallo ta 800 ranar Talata a kungiyoyin da ya buga wa kwallon kafa har da tawagar sa ta kasar Portugal.

A ranar Talata Mancheester United ta je Sifaniya ta doke kungiyar kwallon kafa ta Billareal da ci 2-0 a wasa na biyar na cikin rukuni a Champions League kuma Cristiano Ronaldo ne ya fara ci wa United kwallo a minti na 78, sannan dab a tashi daga karawar Jadon Sancho ya zura ta
biyu a raga. Da wannan sakamakon Manchester United wadda ta kori Ole Gunnar Solskjaer
ranar Lahadi ta kai zagaye na biyu a gasar Zakarun Turai ta bana kenan matakin da a shekarar da ta gabata ta kasa tsallakewa.

Kwallon da dan wasa Cristiano Ronaldo ya ci ita ce ta 800 da ya zura a raga a kungiyoyin da ya buga wa wasa da kuma tawagar Portugal kuma a halin yanzu dan wasan yana da shekara 36 a duniya. Ga jerin lissafin kwallo 800 da Ronaldo ya ci a sana’arsa ta kwallo: Spoting Lisborn ya ci mata kwallo biyar, Manchester United ya zura kwallo 128 a raga, Real Madrid ya ci mata kwallo 451. Jubentus ya zura kwallo 101 a raga. Tawagar Portugal ya ci mata kwallaye 116.

Dan wasa Ronaldo ya fara cin kwallo a kungiyar Sporting Lisborn, ya kuma ci ta 100 a Manchester United, yayin da ya zura ta 200 da ta 300 da ta 400 da ta 500 da kuma ta 600 a Real Madrid. Ronaldo ya ci kwallo ta 700 a lokacin wasan da Portugal ta yi da tawagar
‘yan wasan kasar  Ludembourg a Oktoban shekara ta 2019, yanzu ya zura ta 800 a raga a gidan Billareal a kungiyar Manchester United.

Haka kuma kwallon da ya ci Billareal itace ta 140 a gasar Champions League shi ne kan gaba a wannan bajintar sai dai Shin ko Ronaldo zai amsa CR8, bayan da aka kira shi da CR7 a lokacin da ya zura kwallo ta 700 a tarihinsa.

Exit mobile version