Connect with us

WASANNI

Ronaldo Zai Bude Sabon Otel A Faransa

Published

on

Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Jubentus Cristiano Ronaldo ya bayyana cewa zai bude sabon Otel mai suna CR7 a babban birnin kasar Faransa, Paris kuma shine na shida da dan wasan zai bude a kokarinsa na fadada kasuwancinsa.

A yanzu dai dan wasan yanada guda biyu a Portugal guda biyu daya a kauyensu Punchel yayinda kuma dayan yake a babban garinsu Madeira sannan kuma yana shirin bude wani a babban birnin kasar wato Lisbon.

Har ila yau dan wasan yanada shirin bude wasu a birnin Madrid da kasar Amurka da kuma garin Marekkeh dake kasar Morocco duk domin fadada kasuwancinsa da yakeyi bayan kwallon kafa.

Yanzu dai tuni shirye shirye sunyi nisa domin bude sabon Otel din wanda za’a samu dakuna 210 wanda za’a bude shi a yankin Siena Riber dake kudancin birnin na Paris birnin da yake yawan samun baki ‘yan yawan bude ido daga sassa daban daban na duniya.

Kamar ragowar Otel Otel din daya bude, wannan ma hadin gwuiwa ne da kamfanin Pestana wadanda da hadin gwuiwarsu aka bude ragowar guda biyar din kuma kowanne bangare zai dauki kaso hamsin na kudin da zai kawo.

“Kamar yadda kowa yake jira, Otel din CR7 zai sake bude wani reshen a Birnin Paris na kasar Faransa domin dai ganin mun fadada kasuwancinmu tare da abokan hulda ta” in ji Ronaldo a shafinsa na twitter.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: