Kociyan kungiyar real Madrid, zinedine zidane yace dan wasan gaba na kungiyar, Cristiano Ronaldo, bayajin dadi saboda har yanzu baici kwallo ba cikin wasanni biyu daya bugawa kungiyar sai dai kociyan yace dan wasan zai farfado da cin kwallaye nan bada dadewa ba.
A ranar larabar data gabata ne dan wasan yadawo yiwa Madrid din wasa bayan da aka dakatar dashi wasanni biyar inda yafara da wasan da kungiyarsa tasha kashi har gida a hannun Real Betis a wasan tsakiyar sati da suka buga.
Real Madrid dai har yanzu bata samu nasara a gida ba a wasanni uku data buga inda tabuga canjaras a wasanni biyu sannan tayi rashin nasara a wasa daya.
Sai dai zidane din yaci dan wasan baya jin dadi saboda baya cin kwallo, amma kuma zai dawo da karkashinsa sosai domin daman aikinsa shine cin kwallo.
A ranar talata ne tawagar yan wasan real Madrid din zasuyi tattaki zuwa kasar jamus domin fafata wasa da kungiyar Borussia Dortmund a wasan zakarun turai.
Ronaldo dai yana cikin yan wasa uku da hukumar kwallon kafa ta duniya ta ware domin zama gwarzon dan wasan duniya inda za’a fitar da mutum daya tsakaninsa da Messi da Neymar.