Abba Ibrahim Wada" />

Ronney Ya Yi Ritaya Daga Buga Kwallo Kuma Ya Zama Cikakken Mai Koyarwa

Ronney

Shahararren dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United da Ingila, Wayne Rooney ya yi murabus daga buga wasan kwallon kafa a ranar Juma’ar data gabata, inda ya karbi aikin horar da kungiyar kwallon kafa Derby County wadda take kasar Ingila.

Derby ta tabbatar da nada dan shekara 35 din a matsayin kocinta, inda ta ce ya sanya hannu a kwantiragin din-din-din, bayan da ya maye gurbin Phillip Cocu a matsayin mai koyarwa na wucin gadi a watan Nuwamban shekarar data gabata sakamakon gazawar tsohon mai koyarwar dan kasar Holland wajen samun nasara.

Sanarwa daga kungiyar ta ce amincewa da karbar wannan aikin na nuni da cewa Rooney ya rataye takalmansa na buga kwallo domin ya mayar da hankali a kan aikin nasa kuma kungiyar ta bayyana cewa aikin da tsohon dan Everton din  yayi a kungiyar tun bayan karbar aikinsa shine yasa shugabannin kungiyar sukaga yakamata ya zama mai koyarwar da ‘yan wasan kungiyar gaba daya na din-din-din.

Rooney ya jagoranci kungiyar kwallon kafa ta Derby County buga wasanni 9 a matsayinsa na mai koyarwa amma na wucin gadi, ya lashe wasanni uku sannan ya yi canjaras a wasanni hudu inda ya fitar da kungiyar daga cikin wadanda ake tunanin zasu iya faduwa zuwa ajin kasa.

Rooney ya ce kokarin Derby ne ya ja hankalinsa tun da ya isa kungiyar bayan da ya bar Manchester United, shi ya sa ya ci gaba da zama a cikinta kuma yana fatan shugabannin kungiyar zasu bashi hadin kai yadda yakamata domin ganin ya farfado da ita daga halin da ta shiga a kwanakin baya kafin ya karbi aikin.

Rooney ya zura kwallaye 253 a kungiyar kwallon kafa ta Manchester United wanda hakan yasa yafi kowanne dan wasa a tarihin kungiyar zura kwallo a raga tun lokacin daya koma kungiyar daga Everton a shekara ta 2004.

Har ila yau Rooney ya buga wasanni 559 a Manchester United wanda shine adadi mafi yawa da wani dan wasa ya buga a kungiyar sannan ya lashe gasar firimiyar Ingila guda biyar da gasar cin kofin zakarun turai na Champions League guda daya.

Har ila yau dan wasan ya lashe gasar cin kofin Europa a shekara ta 2017 a lokacin tsohon kociyan kungiyar Jose Mourinho sannan kuma ya sake lashe gasar cin kofin kalubale na FA a lokacin Luis Ban Gaal a Manchester United.

A cikin tawagar kasar Ingila kuwa tsohon dan wasan na Manchester United ya buga wasanni 120 a cikin tawagar ta Birtaniya a karkashin masu koyarwa daban-daban sannan ya zura kwallaye 53 a raga.

 

Exit mobile version