Ɗan wasan baya na Manchester City, Ruben Dias, ya sanya hannu kan sabon kwantiragin shekaru biyu a ƙungiyar.
A baya, kwantiraginsa zai ƙare a shekarar 2027, amma yanzu zai ci gaba da zama a Etihad har zuwa 2029, tare da zabin ƙarin wata shekara idan buƙatar hakan ta taso.
- ’Yansanda Sun Kama Jagororin ‘Yan Bindiga A Abuja, Sun Ƙwato Makamai Da ₦7.4m
- Hukumar Kwastam Ta Kama Kayan Maye Na Miliyan 680 A Katsina
Dias, ɗan ƙasar Portugal mai shekaru 28, ya koma City daga Benfica a 2020 kan kuɗi fam miliyan 65.
A kakarsa ta farko ya lashe kyautar gwarzon ɗan wasan Firimiyar Ingila, sannan a shekaru biyar da ya shafe a ƙungiyar ya taimaka wajen lashe kofunan Firimiya guda huɗu, Champions League, EFL Cup da kuma FA Cup.
Ya ce: “Na yi matuƙar farin ciki a yau. Na saba da Manchester, yanzu ta zama tamkar gidana. Ina matuƙar son magoya bayan City. Idan na tuna nasarorin da muka samu, da kofunan da muka lashe, sai na ji cewa ba zan iya buga wasa a wata ƙungiya ba.”
Daraktan Manchester City, Hugo Viana, ya kira Dias da “jigo a filin wasa.”
A cewar rahotanni, kungiyar na iya mayar da hankali kan makomar wasu ‘yan wasa kamar John Stones da Bernardo Silva, waɗanda kwantiraginsu ya rage shekara guda.
Haka kuma Ilkay Gundogan da Ederson kwantiraginsu ya rage ƙasa da shekara guda.
Sauran ‘yan wasa irin su Rodri, Phil Foden, Manuel Akanji da Nathan Ake duk kwantiraginsu ya rage shekara biyu.