Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home ADABI

Rubutu Da Marubuta: Karance-Karance Da Kallace-Kallace

by Tayo Adelaja
October 7, 2017
in ADABI
5 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
  • Duba gabanka ka ga furanni ma su kyau?
  • Duba bayan ka, ka ji shiru?
  • Kalli damanka ka ga ruwan shayi ko na lemu?
  • Kalli hagun, ka ga littafai?
  • Idan duka amsar ba eh ba ce, gyara zaman ka!

Babu shakka waɗannan kalmomi ba daɗin karantawa kawai gare sub a, a’a shawara ce mai kyau gare mu, tare kuma da nusar da mu muhallin da mu ke buƙata yayin da mu ke shirin samar da wani abu mai alfanu ga al’umma, hususan a rubutu. Wannan kamar mashinfiɗi ne da zan shimfiɗa bayani a game da ƙirƙirar sabon abu.

Gaba ɗayan mu mun yarda cewa shi marubuci mutum ne ma’abocin ƙirƙira. Wato shi mutum ne da aka sani da halayyar samar da sababbin abubuwa. Abubuwan da babu su. Abubuwan da ba a san su ba. Abubuwan da wataƙila mu ka yi imani daga wurin wannan marubuci mu ka fara karɓarsu a matsayin sabon abu. Kodayake a addini bidi’a ɓata ce kai tsaye. Shi kuma ɓata babu tantama haramci ne da ka iya jefa mutum a wuta ranar sakamako, amma a babin rubutu ba haka abin ya ke ba. Babban sinadarin da rubutu da marubuci ke buƙata domin kai sumame tare da mamaye duniyar mabiyan sa shi ne Bidi’a. Eh, bidi’a, ma’ana sabon abu ba. Ita ce babban sinadari, kuma makami mai matuƙar kaifi wanda da shi marubuci kan ci duk bataliyar da ya tunkara da yaƙi. Kuma da bidi’a ne kawai ake amfani wurin sanya marubuci a mizani domin tabbatar da sahihancin fasahar sa, mai biyewa wannan sinadari na bidi’a shi ne SALO, shi kuma wani babi ne mai zaman kan sa, da za mu waiwaya a gaba kaɗan.

Kamar yadda na faɗa ita dai bidi’a ba komai ba ne face sabon abu. Don haka akwai bukatar samar da sabon abu yayin rubutu wanda zai zamto tamkar maganaɗisun da zai fizgi zuciyar makaranci ta yadda zai kwaɗaitu da abin da ke ƙunshe a cikin abin da ya ke karantawa. To amma akwai wani lauje a cikin naɗi. Shin menene ra’ayin masana a kan samar da sabon abu yayin rubutu? Masana da yawa sun yi tambihi a kan cewar, babu wani mutum da zai samar da wani sabon abu wanda ba a taɓa samar da shi ba a baya, ma’ana duk abin da mu ke gani a wannan duniya ba ma a fagen rubutu kawai ba, to tarihi ne kawai ya ke maimaita kan sa, don haka kawai su k ace; fasahar ƙirƙirar marubuta ta ta’allaƙa ne kacokam a tafarkin nazartar hajojin takwarorin sa da ke sassa daban-daban. Wannan wata fatawa Kenan mai zaman kan ta, akwai kuma fatawar da ta yi ittafaƙi kan cewar kowanne marubuci ya na bukatar tasa sabuwar fasahar idan har ya na so ya zama zakaran gwajin dafi. In da su ka buga misali da wani abu da ake kira (Core-Competence) a turance.  Ita dai wannan kalma abin da ta ke nufi shi ne, wani abu fitacce da mutum zai fita zakka da shi a fagen harƙallar sa, ta yadda shi kaɗai ne kacal ke amfani da wannan harƙalla a ko ina aka gani. Ma’ana ya zaman akwai wani Salo da ka ke da shi, wanda ya bambanta ka da sauran. A nan ma zan sake jaddada ma na cewa za mu waiwayi salo a nan gaba kadan.

A hakikanin gaskiya, a cikin waɗannan fatawoyi guda biyu, ko kuma in ce ra’ayoyi na shehunnan malamai a fannin ƙirƙira, ra’ayin da ya fi sahihanci shi ne, abu ne mai wuyar gaske, marubuci ya iya samar da wani sabon abu wanda ba a taɓa samar da shi ba, sai dai ya iya zuwa da wani sabon salo, wanda wani bai taɓa zuwa da shi ba, wannan ɗin ma abu ne mai wuyar gaske, sai dai kamar yadda kalma wuya ta ke a ma’ana, a iya samun wani mai fikirar da zai iya zuwa da salo mai ban mamaki. To tun da dai abu ne mai wuya marubuci ya zo da wani abu sabo wanda bai taɓa wanzuwa ba, shin menene mafita? Mafitar ita ce yawaita karance-karance, da kuma kallace-kallace. Da yawan mu za mu yi mamakin shin menene a cikin karance-karance da kallace-kallace da har ake buƙatar marubuci ya yawaita su?

A shawarce, idan marubuci zai yi rubutu a kan wani labari da ya ke da sarƙaƙiya, da yawan wasa da ƙwaƙwalwa, ko da ace ya na da labarin tun daga farko har ƙarshe, to ya na da kyau ya yi karance-karancen littafai ma su dangantaka da irin wannan labari da ya ke da shi kafin ya rubuta na sa. Hakan ba ya nufin zai wanko abin da ke cikin waɗannan littafai ya zuba a cikin na sa, a’a karantawar za ta haska ma sa abubuwa ma su tarin yawa, kuma tunanin sa zai faɗaɗa ta yadda idan ya samar da na sa labarin zai zama zakaran gwajin dafi. Haka abin ya ke ga rubutun fim, ko waƙa da sauran rukunan rubutu daban-daban. Kowanne sashi mutum zai yi rubutu a kai, akwai buƙatar ya fara lazimtar irin sa daga waɗanda suka gabace shi, da wannan zai inganta aikin sa ƙololuwa. Tare da wannan tunani za mu fahimci cewa babu shakka marubuci ba ya buƙatar lallai sai ya halicci wani abu da babu shi, abin da kawai ya ke buƙata shi ne sabunta tunanin sa a game da abubuwan da mutane su ke kallo ba tare da zurfafa tunani a kan su ba.

Marubuta da yawa da suka yi nasara a faggen rubutu sun sha faɗar cewa mafi akasarin lokutan da za su yi rubutu tunanin farko da ke zuwa gare su shi ne, shin wacce irin kwaskwarima zan iya yi wa wannan labarin domin ya fito a siffa ta daban saɓanin wadda aka saba ji ko gani? Wannan tambaya ta na da matuƙar muhimmancin gaske. Domin wanann tambaya ita ce tamkar masakin linzamin tumbatsar rubutun. Kar marubuci ya narke a wurin ɗaya ko kuma a cikin kogin saƙe-saƙe da tunanin sai ya halicci wani abu da babu shi, domin yin hakan kai tsaye ya na toshe ƙofofin balagar sa ne a matsayin sa na marubuci.

Satar fasaha ko kaɗan ba ta dace da abin da na ke nufi a nan ba. Kamar yadda mutane da yawa su ka sha faɗar cewa bai kamata marubuci ya kwaikwayo wani labari daga wani wuri ba, kuma har suna ganin sa a matsayin laifi. Babu shakka kwaikwayon wani abu daga wani wuri ba laifi ba ne, har a duniyar rubutu. Sai dai ya ragewa shi mai kwaikwayon ya sarrafa wannan abu da ya kwaikwayo daga wata al’umma ko wata nahiya, ya mayar da shi daidai da irin na ta sa al’ummar ba tare da tauyewa ko salwantar da haƙiƙanin saƙon ba. A ƙarshe ya kamata mu sani, da ba don kwaikwayo ba da abubuwa da yawa ba su yiwu ba, a cikin har da kayan more rayuwa da na ingantawa da muke amfani da su a yau da gobe. Komai ya fara ne daga kwaikwayo, kuma zai ƙare ne daga kwaikwayo.

Bissalam!

 

Tare da Nazir Alkanawy 08035638216            imel: naziralkanawy@gmail.com.

SendShareTweetShare
Previous Post

Murtala Mai-Sallah: Tun Muna Ƙanana Mahaifinmu Ya Ɗora Mu A Turbar Kasuwanci

Next Post

Babban Burina Duk Bayan Wata Biyu Na Ƙera Sabbin Na’urori — Adamu Husawa

RelatedPosts

M. Haris Hotoro

Dalilina Na Koma Wa Rubutun Fim Daga Na Litattafai – M. Haris Hotoro

by Sulaiman Ibrahim
5 days ago
0

Matashin marubucin littattafan Hausa da ake wa lakabi da M....

Littafin

SHARHIN LITTAFI: Littafin Koyon Salatin Annabi Cikin Sauki

by Muhammad
2 weeks ago
0

Daga Ibrahim Sheme, SUNA: Salatin Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wa...

Waka

Idan Waka Na Cin Zabe, Mamman Usman Zai Lashe Zaben Kasar Nijer – Kosan Waka

by Muhammad
4 weeks ago
0

MUHAMMADU BUHARI shine da aka fi sani da KOSAN WAKA...

Next Post

Babban Burina Duk Bayan Wata Biyu Na Ƙera Sabbin Na’urori — Adamu Husawa

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version