Tare da Nazir Alkanawy
08035638216 imel: naziralkanawy@gmail.com
Kamar yadda muka sani kowanne abu ya na da lokacin sa, da yawan mu kuma mun yarda cewa idan aka yi abu a lokacin da ba na sa ba ya kan ɓaci, wani zubin ma ya lalace gaba ɗaya. Kuma mun rigaya mun san abubuwa da yawa ba sa wanzuwa sai lokacin su ya yi, takurawa sai sun farun ba tare da lokacin na su ya yi ba, ya kan haifar da gagarumar matsala, musamman a rayuwar mu ta yau da gobe.
Ga misali yadda za a fahimta; Idan ka zauna ƙememe ka ƙi cin abinci tsawon wuni guda alhali lokacin cin abincin ya yi, nan take gangar jikin ka za ta fara gaya ma ka cewa ka na cutar da ita, kowacce gaɓa za ta fara ɗaukar mataki na neman agajin gaggawa, cikin ka ya fara juyawa ya na karta, idanun ka su fara disashewa ka rinƙa gani sama-sama, kan ka ya fara ciwo nan take, haka nan gaɓoɓin da ke bayar da kuzari gare ka duka za su gaza, alamu da ke sake jaddada ma ka cewa lallai fa ka na buƙatar sauke hakkin su ka ba su sinadarin ci gaba da wanzuwar su.
Ko shakka babu rubutu ya na buƙatar nutsuwa da keɓewa daga cikin hayaniyar mutane yayin gudanar da shi. Idan kuwa har haka ne, lallai akwai buƙatar samar da lokacin gabatar da shi, lokacin da marubuci zai samu kan sa a cikin nutsuwa, domin samun faragar samar da sabbin abubuwa. To amma marubuta sun kasu gida-gida, rukuni-rukuni, ko kuma a sauƙaƙe in ce kusan kowanne marubuci ya na da bambanci da dan uwan sa, abin da ke birge wannan ba shi ke birge wancan ba, abin da wannan ke jin daɗin sa babu mamakin wancan kuma azabtar da shi ya ke yi. To tun da haka abin ya ke ta yaya Kenan za a samar da lokacin da ya dace a yi rubutu? Shin wanne lokaci ne ma fi dacewa domin samar da rubutu?
Kafin na gangara zuwa gwadaben amsa wannan tambaya, zan so fayyace ma na wasu muhimman abubuwa guda biyu da ke wahalar da duniyar kowanne marubuci, waɗannan abubuwa su ne “Buƙatar yin rubutu” wanda ake kiran sa da (Inspiration) a harshen nasara, sai kuma abu na biyu wanda ake kiran sa “Toshewar basirar marubuci” a harshen nasara kuma sunan sanan sa na yanka shi ne (Writers Block) Wato ko daga jin Kalmar an san wani abu ne da ya ke da alaƙa da doɗewar basira da ƙwaƙwalwa illahirin ta. Abu na farko wato (Inspiration) a sauƙaƙe ya na nufin yanayin da marubuci kan tsinci kan sa cikin basira da iya ƙirƙira nan take. A wannan yanyi ƙwaƙwalwar marubuci ta na da sauri, kuma tunanin sa ya na da kaifi da kuma zurfi. Duk abin da ya ke buƙata nan ta ke ya ke samar da shi. Saɓanin na biyun, wanda shi kuma kishiya ne ga na farkon. Ma’ana yanayi ne da marubuci ya ke kasa ƙirƙirar komai, a wasu lokutan idan marubuci ya shiga wannan yanayi (Writers Block) Ya kan fassara kan sa a matsayin mutum mafi rashin basira, sakamon bijire ma sa da dukkan ƙofofin ƙirƙirar sa ke yi su kulle gaba ɗaya.
Waɗannan yanayi guda biyu su na da siffofi daban-daban ga marubuta daban-daban. Wani da zarar ya saurari tattausar waƙa sai ya sa mu (Inspiration) na yin rubutu, wani sai ya kalli fim, wani kuma sai ya yi karatu, wani Sai ya hau kan masai ya ke samun na shi (Inspiration) din. Wata sai ta ɗora tukunya a kan murhu za ta fara girki tukunna. Wata kuma sai an kama kan ta za a yi ma ta kitso. Wata sai ta na cikin hira da mijin ta, wata kuma sai dare ya tsala ta ji kowa ya yi shiru ƙafafu sun ɗauke. Ga su nan dai birjik!
Don haka kowanne marubuci na sa yanayin daban ya ke da na ɗan uwan sa, yanyin da wanna ke da basira ta iya yiwuwa shi kuma wancan tasa a toshe ta ke, don haka kowanne marubuci ya na buƙatar ya san shin wanne yanayi ne ya ke da (Inspiration) na yin aiki? Kuma wanne yanayi ne ya ke afkawa tarkon (Writers Block)? Idan ya samu amsoshin waɗannan tambayoyin biyu, to shikenan sai kuma ya tsallaka zuwa waccan tambayar ta farko da na baro. Shin wanne lokaci ne ya dace da rubutu? To amsar wannan tambaya itama ta bambanta ga kowanne marubuci. Yanayin marubuci yanayin lokacin da ya ke buƙata domin yin rubutu. Don haka babu wanda zai amsa ma sa wannan tambaya face shi kan sa. Shin yaushe ka fi samun (Inspiration)? Ko kuma menene ya fi ba ka shi (Inspiration) din? Kuma menene ya ke haifar ma ka da toshewar basira (Writers Block)?
Da yawan marubuta gajiya ce ke haifar mu su da toshewar basira. Wani kuma ɓacin rai ne ke haifar ma sa da wannan matsala, wani kuma tsabar tarin aiyukan da suka gabata ne a gare shi. Kowanne dai akwai dalilin samun ta sa matsalar toshewar basirar. Idan marubuci ya fahimci lokacin da ya ke iya ƙirƙirar rubutu, sai ya alkinta wannan lokaci ya zamar ma sa shi ne lokacin da ya fi yin rubutu, domin a yawancin lokuta ba sai ka na da (Inspiration) za ka yi aiki ba, marubucin gaske, shi ne ya san hanyar da ya ke yin rubutu ko da ba shi da (Inspiration) din, har sai ya samar da shi da ƙarfin basirar da ya ginawa kan sa ta musamman.
Haka ma matsalar toshewar basira, yayin da marubuci ya tsinci kan sa a ciki, ba shi da zaɓin da ya wuce ya ajiye rubutun zuwa wani lokaci. Sannan zai fi kyautuwa ya gayyato duk wasu abubuwa da su ke iya tuna ma sa wata rayuwa mai armashi da ya taɓa tsintar kan sa a cikin ta, hakan zai taimaka ma sa ainun wurin dawo da basirar ta dawo sabuwa fil! Amma fa ya na da kyau kowanne marubuci ya sani, babu wani lokaci da ya fi dacewa da rubutu fiye da lokacin da aka rasa hayaniyar mutane. Sannan babu wurin da ya dace da rubutu fiye da wurin da ke da yalwar shiru, kyawawan furanni ma su kyawu da kuma yalwar shuke-shuke koraye, sai kuma kukan tsuntsaye ma su daɗi, haƙiƙa irin wannan muhalli ya kan ba wa marubuci damar hararo shekaru ɗari da suka gabata da kuma shekaru ɗari ma su zuwa…