Tare da Nazir Alkanawy 08035638216 imel: naziralkanawy@gmail.com
Tare da sallama gami da gaisuwa mai yawa, barkanmu kuma lale marhabin da sake gamuwa da juna a wannan shafi na mu mai sarkakiya kuma sassauka wato Rubutu da Marubuta.
Kamar yadda taken rubutun na mu na yau ya nuna, wato Marubuci da Nazari za mu duba dangantakar da ke tsakanin Rubutu da kuma Nazari. Shin menene ya sanya na goya Kalmar Nazari da Kalmar Marubuci ko kuma na daura aure a tsakanin kalmomin biyu?
To da farko dai akwai dangantaka mai karfin gaske a tsakanin kalmomin guda biyu, ko kuma in ce Danjuma ne da Danjummai. Daga nazari ne aka samu rubutu kamar yadda manazarci ne ke rikida ya koma marubuci. Marubucin da ba ya nazari ba za a iya kiran sa da marubuci ba kai tsaye. Domin sarrafa tunanin da aka nazarto a rubuce, shi ke haifar da marubuci har ya kai mizanin balaga. To wai shin ita Kalmar nan ta nazari, mecece ita? Ko kuma kai tsaye mu ce, me ake nufi da nazari a ilmance? Shi nazari ya na farawa ne daga tunani, kamar yadda masana kimiyyar Dan’adam da tunanin sa (Psychologist) suka rawaito cewa kowanne dan’adam a cikin tunani ya ke, daga ranar haihuwarsa, har zuwa ranar mutuwarsa. Wannan haka ya ke, ko da mun sani, ko da ba mu sani ba, dukkan mu a cikin tunani mu ke, a kowacce dakika da ke harbawa, a cikin awanni ashirin da hudu da ke cikin kowacce rana, a cikin tunani mu ke. Wannan kadan kenan daga hikima irin ta Ubangiji Allah buwayi gagara misali.
Daga wannan tunani, dan’adam ke zurfafawa zuwa nazari. Shi kuwa nazari kacokaf ya ta’allaka ne a kan jajircewa a wani tunani da ya gilma kwakwalwa tare da tilastawa har sai an samu sakamakon da ake bukata a kan shi wannan abin da ake da muradi.
Dauki misalin kana tafiya a kan hanya, sai ka ci karo da wasu ‘yan mata guda biyu suna fada a tsakaninsu a kan titi, kuma fadan a kan saurayi ne; watakila tunaninka zai iya ba ka cewa daya daga cikin ‘yan matan ce ta yi wa ‘yar uwar ta kwace, kuma a nan take, za ka yanke hukuncin ba wa wadda ta yi kwacen saurayin laifi. Wannan a fannin tunani kenan, amma a fagen nazari ba haka abin ya ke ba! Kwarai da gaske ba haka abin ya ke ba domin kuwa da ka zurfafa cikin nazari watakila za ka gane cewa ba lallai wadda ka ke zaton ta yi kwacen saurayi ya kasance kwacen ta yi ba. Babu mamaki saurayin ne ya ke bibiyar ta, watakila ma ita ba ta karbi tayinsa ba. Daga nan za ka fara kokarin yi wa kowa adalci a cikinsu, wannan gabar kuma to ka fara kirkirar labari ba tare da ka sani ba, a kokarin ka na yi wa kowa adalci za ka fara hasashen gaskiyar kowanne wanda kuma dalilin haka za ka fara kokarin waiwayen rayuwar wadannan mutane da ta gabata. A waiwayen ne kuma za ka hada zarrrukan labari ma su ban sha’awa da ban mamaki, watakila su birge ka, idan kuwa har sun birge ka, to za su birge duk wanda ya ji labarinka.
Na san babu mamaki ka fara zancen zuci a halin yanzu, ka na tambayar kanka cewa to me ya sa za ka zurfafa da bincike a kan labarin wasu da ba su shafe ka ba, a titi kawai ka hadu da su? To ga amsarka: kaso ma fi tsoka na labaran duniya sun faru ne daga bibiyar rayuwar wadanda ba su shafe ka ba. Kaso ma fi tsoka na marubutan da suka kware wurin sarrafa labarai, kuma suka mallaki zukatan makarantansu sakamakon dandanon labaransu ma su armashi, sun samo wannan sirrin ne da ga shisshigin shiga rayuwar wasu mutane da ba ta shafe su ba. Ke nan duk mai son zama cikakken marubuci, sai ya zama ma’abocin nazari, a tafarkin nazarin kuma sai ya zama ma’abocin shisshigi da shiga sharo-ba-shanu, duka dai domin farauto labarin da zai kama zuciyar al’umma. Kuma fa wannan ita ce ribarka a matsayinka na marubuci, idan ka kama zuciyar makaranta, ka kama zuciyar al’ummarka da ma wadda ba taka ba; ko babu sisi a tare da kai, burinka ya cika, kuma bukata ta biya. Da ma dai bukatar maje-hajji sallah, kuma ya yi har ma da nafila!
Ya zama wajibi marubuci ya iya nazari. Kuma tilas ne ya kasance a koyaushe a cikin nazari. A hakikanin gaskiya, ba komai ya kamata ka kalla ka dauke kai ba, wani abin ya na bukatar duba na biyu har na uku, wani abin kuwa duba na tsanaki ya ke bukata; duba na tsanaki kuwa magana ce ta duba barkatai, babu adadi har sai an samu abin da ake bukatar sani. Ba kasafai manazarci ya ke saka matoshin kunne (Headphone) ya toshe kunnensa ya na sauraron kida ba, a’a ya kan bar kunnuwan sa a bude, haka ma idanunsa sannan kofofin zuciyarsa a bude suke fayau, kwakwalwarsa ba ta zaman alkalanci da yanke hukunci a game da abin da ta ga wani aikata, sai dai kulafucin neman dalilai da suka haifar da faruwar wannan abu da aka aikata, ta haka ne da sannu manazarci zai samu ingantattun abubuwan fada, wadanda su ne labarai ma su bugun zuciya nan take, ba tare da ya shirya ba sai ya ji sunansa a matsayin marubuci yana ta yaduwa har sai duniya ta gamsu da shi, tana yi ma sa maraba a duk lokacin da ya bude baki zai yi magana, ko kuma ya dauki alkalami zai yi rubutu, da sannu sai mutane sun fara tururuwar siyan rubutunsa domin amfana, wanda duka nazari ne ya haifar da shi.
Dauki misalin motar haya, ko da ka na da abin hawa, ajiye shi ka shiga motar hawa. Ka kalli mutane daya bayan daya, za ka ga kowa launin fuskarsa ta bambanta da ta dan’uwansa, mata da maza, yara da manya har ma da tsofaffi. Wadannan mutanen da kake gani, kowa rayuwar sa labari ce. A cikin wadannan mutanen, zabi mutum daya wanda ya fi jan hankalinka. Ka kare masa kallo irin wanda ba zai cutar da shi ba, sannan sai ka fara ayyana rayuwarsa a ranka, ka kirkirar masa mata, wadda ya sha gwagwarmaya kafin auren ta, suna da ya guda daya, ko biyu. A halin yanzu ya fita nema bai samu ba, don haka ya na cikin fargabar isa gida ba tare da abin kaiwa bakin salati ba. Ka ayyana ana bin sa basussuka, kuma sana’ar da ya ke yi ya na fuskantar barazanar rasa ta. Don haka ya na cikin damuwar sauya wata sana’ar kuma bai san ta ina zai fara ba…
Daga haka ka gina masa labari, kuma watakila idan ka bincika tarihinsa, sai ka ga abubuwa da yawa da ka ayyana haka su ke. Wannan daya daga cikin shu’umancin nazari kenan. Daga haka ka fara gina labari, kuma wannan bawan Allah shi ne jarumin labarinka.
Rubutu ya na da wani sharadi, sharadin kuwa shi ne; ya zama wajibi duk abin da za ka rubuta ya zama ya na kamanceceniya da rayuwar al’umma ta zahiri, sai dai idan har almara kake bukatar kirkira, wannan kuwa kowa ya san wani abu ne da bai yi kama da rayuwa ta zahiri ba.
Da taimakon nazari ake samun ingantaccen rubutu. Da mai sha’awar fara rubutu, da wanda ya ke cikin duniyar rubutu, ya zama wajibi mu sani, dole ne mu inganta dabi’ar nazartar abubuwa. Yawancin abubuwa ba yadda suke muke kallon su ba, sai mun kusance su, mun kare masu kallo tare da yi mu su adalci a hakikaninsu, sannan ne mu ke fahimtar su ainahin fahimta.
Ba kowanne abu ne za ka kalla ka dauke kanka ba. Kar ka ji labarin wata ta yi cikin shege kawai ka tsine mata, ka ci gaba da harkokinka, a’a yi tunani a kanta. Ka ayyana yadda kake zaton rayuwar macen da ta yi cikin shege za ta kasance. Sai kuma ka fara tunanin sababin cikin shegen, soyayya ce? Ko bacin rai? Rashin gata ne ko kuma kawai son zuciya ne? Ko kuma a’a kawai burinta ta yi cikin shege shi ya sa ta je ta gayyoto abokin cin mushe suka aikata wannan ta’asa? Irin wadannan tambayoyin da samun amssoshinsu, za su kaifafa imaninka, sannan za su kaifafa kwakwalwarka wurin samar da labarai masu taba zuciya. Ko labarin fim za a rubuta, ko na littafi, ko na waka, akwai bukatar wanda zai rubuta ya tafi nazarin dabi’un mutane, ya zabi wadanda suka fi birge shi, ya jingina labarinsa da su, ya yi wa labarpn kwaskwarima, sannan ya rubuta shi cikin la’akari da wannan mutane da ya nazarta, ko shakka babu idan aka gama labarin, mutane za su yi dokin dandanon labarin domin ya na kama da rayuwarsu, wasu da yawa ma za su ji kamar da su ake, kuma a zahiri ba da su din ake ba. Idan mutane su ka ji haka, to labari ya yi nasara, kuma sako ya isa.
Muhimmin abu ga rubutu shi ne, mutane su tsinci kansu a duniyar wannan labari, har ta kai idan wani abu ya samu jaruminsu mara dadi, suna taya shi alhini, haka idan alheri ne su taya shi murna.
Akwai lokuta da yawa muke kallon fim mu yi kuka, ko mu na karanta littafi mu kyalkyale da dariya, hakan ta kan faru ne yayin da muke jin mu a cikin wannan duniya da labari ke faruwa.
Zan sake jaddadawa, dole ne nazari ya zama babban abokin marubuci, ya zama bacci ne kawai yake raba su, in son samu ne ma, a baccin, ya zurfafa wurin nazari ta hanyar kirkirar wa kansa mafarki, mai ban sha’awa.
Sai mun sadu a mako mai zuwa.