Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home ADABI

Rubutu Da Marubuta: Salo

by Tayo Adelaja
October 14, 2017
in ADABI
5 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Tare da

Nazir Alkanawy 08035638216           imel: naziralkanawy@gmail.com.

samndaads

A wannan makon kamar yadda na yi alƙawari a baya, za mu waiwayi Kalmar Salo. Ko a suna, mun san salo abu ne da ke nufin gwaninta kai tsaye. To amma da farko kafin mu yi nisa, ya na da kyau mu fara fige kazar Kalmar Salo domin fahimtar ma’anar ta kai tsaye. Shi dai salo a iya cewa ya na nufin tafarkin tura saƙo, ko gabatar da wani abu. Tun da kuwa hanya ce Kenan hanyar nan ta iya yiwuwa mai kwazazzabai, ko kuma mai tudu da gangare, ta iya yiwuwa kuma hanya ce miƙaƙƙiya wadda ko kwana babu, wata kuma hanyar za ta iya kasancewa mai kwana-kwana wadda tun ana tafiya a cikin ta da marmari har sai an zo ana nadamar biyo ta.

Kowacce hanya dai akwai dalilin samuwar ta, kuma akwai ma’anoni a ƙarƙashin ta, sai dai idan ba a bincika an samu ba. Kuma kowanne mutum ya na da yancin zaɓar hanyar da ya ke son bi, domin zuwa wani muhimmin wuri da ya ke hari. Kuma ya rage na sa, ya san ta yadda zai yi tafiya a kan wannan hanya, ko dai ya yi taka-tsan-tsan ko kuma ya yi ta tafiyar sa gaba-gaɗi. Abu mafi muhimmanci da ya kamata mu sani shi ne, kamar yadda kowanne mutum akwai irin tufafin da za su dace da surar jikin sa, haka kowanne marubuci, akwai salon da zai dace da surar ƙwaƙwalwar sa. Kamar yadda masana suka sha faɗa, babu wasu iyakokin salallaki da aka gabatar a matsayin su kaɗai ne hanyar isar da saƙo, mutum ya iya ƙirƙirar sabon salo wanda ba a taɓa yin irin sa ba. Misalai suna nan birjik!

Ɗauki misalin waƙa. Yayin da makaɗi ya zauna domin halittar bushe-bushen sa, da farko zai fara amfani da sauti mara daɗin sauraro, amma sannu a hankali idan ya ci gaba da sarrafa su sai ka ji sun fara bayar da wani sauti mai ma’ana. Idan ka ci gaba da jimirin sauraro babu shakka za ka sha mamakin yadda wannan bushe-bushen marasa daɗi da farko za su rikiɗa su zama ma su daɗin sauraro a kunnuwan ka. Me ya sa? Saboda komai daga farko ba kasafai ya ke da ɗanɗano ba. Sai an sake, an sake sake wa, an sake sakewa.

Haka ma abin ya ke ga mawaƙin da ya fara rera waƙa. Muryar sa wani lokacin ta kan fara ne a dashe, amma sannu a hankali idan ya ci gaba da rerawa muryar sai ta rinƙa feƙewa ta na ƙara daɗi kwatankwacin yadda gwanayen almajirai su ke feƙe gamba ta rikiɗa daga wani katako maras galihu zuwa alƙalamin da ake yin rubutu da shi. Haka ma murya ta ke, a kan feƙe ta ta yi kaifi, kuma ta yi daɗin sauraro, amma ta hanya ɗaya kacal! Wannan hanya kuwa ita gwaji. Idan na ce gwaji ina nufin gwadawa ba sau ɗaya ba kuma ba sau biyu ba. Wataƙila ma sai an gwada ya fi sau shurin masaƙi. To amma dai a sani, a ƙarshe matuƙar an gwada to za a dace. Kamar dai ƙofa ce, matuƙar an ƙwanƙwasa ta, to babu makawa za a buɗe sai dai idan har babu kowa a cikin kofar. A ci gaba da ƙwanƙwasa babu makawa za a buɗe, wannan alƙawari ne daga bakin wanda ba ya ƙarya ko kuskure.

Don haka ga duk marubucin da ke buƙatar tasarifin salo a cikin rubutun sa, to haƙiƙa ya na da kyau ya mayar da hankalin sa ga sautin muryar sa. Idan muryar ka ta na daɗi ka fi kowa sani, haka nan idan ma ba ta da daɗi ka fi kowa sani, domin dai babu wanda ya san ka fiye da yadda ka san kan ka. Ka fi kowa sanin abin da ya fi dacewa da kai, idan ka bincika a hankali za ka fahimci hakan. Idan ka fahimci muryar ka na da daɗi to shikenan sai kawai ka ƙara wa kwalliyar ka armashi da wanka, amma idan fa muryar nan ba ta daɗin sauraro to la-budda akwai buƙatar a sake yi ma ta kwaskwarima da gyaran fuska, wannan kuma abu ne mai sauƙi muddin dai an fahimci hakan. Saura da me? Ya ragewa marubucin da ya fahimci haka ya jajirce a fagen fafutukar feƙe muryar sa, ta kasance mai daɗin sauraro ta yadda idan ana sauraron muryar sa za a shagaltu ba tare da an gaji ko ya gundurarar. Wannan murya da na ke ta Magana a kan ta it ace kalaman da marubuci ya zaɓa wurin isar da saƙonsa da su. Su ne muryar. Da su ake rarrabe daɗi da rashin daɗin wannan muryar. Kowanne marubucin da ya san abin da ya ke yi, ya kan yi wa kan sa waɗannan tambayoyin yayin da zai rubuta kalaman sa.

Wa na ke isar wa da saƙo na?

Me zan faɗa ma sa?

Ta wacce hanya zan faɗa ma say a fahimce ni?

Idan ni na ke sauraron wannan Magana, ya zan ji?

Idan har an amsa waɗannan tambayoyi cikin gaskiya da amana, to babu shakka za a samu sakamako mai kyawu. Wanda ya yi wa kan sa wannan tambayoyi ba tare da ya ba wa kan sa gamsassun amsoshi ba, to haƙiƙa ya ci amanar rubutun sa. Kuma ko shakka babu shi ma rubutun sai ya ci amanar sa. Don haka abu ma fi muhimmanci shi ne kasancewa cikin fuskantar gaskiya a yayin rubutu. Idan muryar ka na da daɗi ka ƙara ma ta armashi. Idan ba ta da shi, ka samar ma ta da shi ta hanyar sauya kalaman ka, tare da yi mu su gurbi a wurin da ya dace da su. Da haka ne kaɗai za ka yi galabar sace zuciyar ma su karatun ka. Da wannan ne kuma za ka zama malami mai koyar da su ba tare da sun shirya ba.

 

Fatan alheri.

 

 

 

SendShareTweetShare
Previous Post

Abubuwan Da Masoya Ba Su So A Lokacin Hira

Next Post

Auratayya

RelatedPosts

Littafin

SHARHIN LITTAFI: Littafin Koyon Salatin Annabi Cikin Sauki

by Muhammad
1 week ago
0

Daga Ibrahim Sheme, SUNA: Salatin Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wa...

Waka

Idan Waka Na Cin Zabe, Mamman Usman Zai Lashe Zaben Kasar Nijer – Kosan Waka

by Muhammad
3 weeks ago
0

MUHAMMADU BUHARI shine da aka fi sani da KOSAN WAKA...

An Karrama Marubuciya Umma Sulaiman Saboda Ayyukan Jinkai

An Karrama Marubuciya Umma Sulaiman Saboda Ayyukan Jinkai

by Sulaiman Ibrahim
4 weeks ago
0

Jajirtacciyar 'yar gwagwarmayar kare mata da kananun yara kuma shugabar...

Next Post

Auratayya

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version