Rufe Iyakokin Nijeriya: Makwabta Na Ci Gaba Da Yin Korafi

Matakin rufe iyakokin da Nijeriya da ta yi tsakaninta da kasashe masu makwabta da ita, na ci gaba da haddasa ce-ce-kuce a tsakanin jama’a. Inda a halin yanzu kasashen suke ci gaba da koka wa bisa rufe iyakokin Nijeriyar.

Yayin da wadansu kuma ke ganin cewa matakin ya dace, wasu kuwa na ganin cewa ya haddasa mummunan sakamako a fagen tattalin arzikin kasar da kuma na makwabta.

A Maradi dake Jamhuriyar Nijar, wacce take a matsayin yankin da ke gudanar da hadada-hadakar kasuwanci ta milyoyin kudade tsakaninta da Najeriya, a halin yanzu ita ma birnin na cikin tsaka mai wuya na koma bayan hada-hadar kasuwanci.

 

Exit mobile version