Sani Anwar" />

Ruga:An Zuba Naira Miliyan 300 A Kano

A cigaba da shirye-shiryen batun samar da shirin Ruga, wanda a ke kyautata zaton zai taimaka wajen inganta harkokin tsaro tare da samar da zaman lafiya a fadin kasar nan bakidaya,  Gwamna Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya tabbatar da sanya Naira Miliyan 300, domin samar da wuraren kwana tare da sauran abubuwan da sojoji ke bukata na horo da kuma samar da wuraren kiwo ga Makiyaya a fadin Jihar.

“Sama da Naira Miliyan 300 mu ka ware domin samar da wuraren kwana da sauran abubuwan  amfanin sojoji, tare da samar da wuri na din-din-din domin gudanar da horo a Dajin Falgore. Sannan, za mu samar da sauran abubuwan da ake bukata ga Makiya, ta yadda za a samar da wuraren kiwo domin amfanin Fulani Makiyaya”, in ji Ganduje.

Gwamnan na yin wanann jawabi ne, a lokacin bikin kaddamar da Cibiyar Harkokin lafiya, wanda aka gudanar a garin Gada-Biyu da ke Karamar Hukumar Doguwa, inda aka sama wa da Runduna ta 78 domin fara aiki, wadda aka sanya wa suna Soja-Kun-Gama da ke cikin Dajin Falgore.

Kazalika, ya kara da cewa, “yana da matukar muhimmacin gaske Jihar Kano, ta samar da wannan wuri, domin  hada kan Jami’an tsaronmu. Sannan, a halin yanzu muna kan kashe makudan kudade domin ganin mun samar da wuri na dindin, yayin da su kuma Makiyaya za su samu wadataccen wurin kiwo.”

Har ila yau, Ganduje ya tabbatar da fatan da ake da shi, na kokarin kakkabe kafatanin ‘yan fashi da masu yin garkuwa da mutane da kuma sauran masu aikata muggan miyagun laifuka. Haka nan, hadakar fararen huluna a cewar Gwamnan, za ta bayar da gagarumar gudunmawa tare da nasara wajen samar da kyakkyawan a fadin wannan Jiha.

Haka zalika, Gwamnan sake ya jaddada cewa, “muna farin ciki kwarai da gaske musamman ganin yadda wadannan Sojoji ke tafiyar da Cibiyar Harkokin Lafiya, domin amfanin al’ummar wannan yanki. Ko shakka babu, wannan abun a yaba ne kwarai da gaske, sannan hakan zai

iya taimakawa wajen samar da kyakkyawar danganta tsakanin wadannan Sojoji da kuma fararen

hula.

Da ya ke gabatar da nasa jawabin, Shugaban Hafsan Hafsoshin Sojojin Nijeriya, Janar Tukur Buratai,  wanda Manjo Janar Enobong Udoh, Shugaban sashin bayar da horo na rundunar Sojan Nijeriya, ya samu wakilta cewa yi, wannan taro babu shakka zai kara samar  da ingantacciyar dangantaka  tsakanin Sojojin Nijeriya da kuma al’ummar Garin Gada-Biyu, da kuma sauran Garuruwan da ke Karamar Hukumar Doguwa.”

Wannan dalili ne ya sanya ya bukaci al’ummar wannan yanki da cewa, ka da su gaza wajen bayar da dukkanin taimako ga Jami’an Soja. “Wannan Cibiya ta lafiyar wadda rundunar Soja  ta samar, na nuna tabbacin ci-gaba da shiga tsundum cikin aiki, domin samar da dukkanin abubawan da ake bukata na Soja, wadanda suka hada da Bataliya da sauran abubawan da za a samar a wurin domin inganta dangantaka tare da tabbatar da kudurin da duniya ke amafani da shi a halin yanzu.”

Har wa yau, Burutai ya sake jinjina wa Gwamna Ganduje, musamman a wajen kokarinsa na  kasancewa a wannan wuri shi da kansa, “babu shakka, zuwanka wannan wuri ya kara haskaka wannan taro kwarai da gaske,” kamar yadda Daraktan Yada Labaran Gwamnan, Abba Anwar, ya shaida wa LEADERSHIP A YAU.

Exit mobile version