Leadership News Hausa
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership News Hausa
No Result
View All Result

Rundunar Barkhane Ta Fadada Aikinta Na Yakar Ta’addanci A Mali

by
3 years ago
in Nahiyar Afirka
1 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
ADVERTISEMENT

Labarai Masu Nasaba

An Dage Ranar Bude Makarantu A Nijer Saboda Ambaliyar Ruwa

‘Yan Kamaru Sun Yi Bore Kan Shugaba Biya Ya Sauka Daga Mulki

ADVERTISEMENT

Bayan shafe tsawon shekara guda da rabi ta na fafutukar samar da tsaro a garin Liptako dake yankin Arewa Maso Gabashin Mali, rundunar musamman ta sojin Faransa “Barkhane”, dake yaki da ‘ya ta’adda a yankin Sahel, ta fadada aikinta zuwa garin Gourma da ke tsallaken kogin Nija, a kan iyakar Mali da Burkina Faso.
Tun a shekarar 2017 Rundunar sojojin Faransar na Barkhane suke yakar gungun mayakan da suka yi wa kungiyar Al’ka’eda mubaya’a a garin Liptako dake kan iyakar Mali da Jamhuriyar Nijar, wanda kuma a yanzu sun cimma gagarumar nasara a cewar Janar Francois Lecointre, daya daga cikin manyan kwamandojin Dakarun na Barkhane, hakan ya sa su fadada aikinsu zuwa Gourma.
A baya-bayan nan dai mayakan masu da’awar jihadi sun kai munanan hare-hare kan sojojin Mali a Garin na Gourma dake kan iyakar Mali da Nijar, sakamakon karfi da mayakan kungiyar Ansarul Islam masu biyayya ga Al’kaeda suke dada samu a yankin na Kudu Maso Gabashin Kasar ta Mali.
A watan Nuwamban bara dakarun Faransa suka hallaka Al Mansour, Shugaban kungiyar ta Ansarul Islam a wani farmakin da suka kai kan garin na Gourma, amma har yanzu mayakan suna ci gaba zama babbar barazana, saboda mafakar da suke samu a dazukan da ke kan iyaka da Arewacin Kasar Burkina Faso.
A shekarar 2012 Mali ta fuskanci barazanar tsaro mafi girma bayan da mayaka masu da’awar Jihadi suka kwace baki dayan yankin Arewacin Kasar, sai dai a 2013 sojojin Faransa na Barkhane suka yi nasarar dakile, amma har yanzu mafi akasarin yankin Arewacin na ci gaba da kasancewa a karkashin mayakan.

Like this:

Like Loading...
SendShareTweetShare
Previous Post

Za A Kafa Sabuwar Gwamnati A Aljeriya

Next Post

An Karrama ‘Yan Wasan Nijeriya ‘Yan Ajin Shekara Ta 1994

Labarai Masu Nasaba

An Dage Ranar Bude Makarantu A Nijer Saboda Ambaliyar Ruwa

An Dage Ranar Bude Makarantu A Nijer Saboda Ambaliyar Ruwa

by
2 years ago
0

...

‘Yan Kamaru Sun Yi Bore Kan Shugaba Biya Ya Sauka Daga Mulki

‘Yan Kamaru Sun Yi Bore Kan Shugaba Biya Ya Sauka Daga Mulki

by
2 years ago
0

...

Garkuwa

Gwamnan Zamfara Ya Bada Umarnin Amfani Da Kalandar Musulunci

by
2 years ago
0

...

Irin Kallon Da Akasarin ‘Yan Kasa Ke Wa Kudirin Kalaman Kiyayya

Sanatoci Sun Amince Da Hukuncin Daurin Rai-da-rai Kan Masu Satar Mutane

by
2 years ago
0

...

Next Post
An Karrama ‘Yan Wasan Nijeriya ‘Yan Ajin Shekara Ta 1994

An Karrama ‘Yan Wasan Nijeriya ‘Yan Ajin Shekara Ta 1994

Leave Comment

Domin bayar da talla ko neman ƙarin bayani a tuntuɓe mu a: +2348039216372

  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us | English Edition | Fashion Magazine | Business News

© 2022 Leadership Media Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2022 Leadership Media Group .

%d bloggers like this: