Rundunar OPSH Ta Kama Masu Warwason Kayan Tallafin Korona A Jos

Warwason

Rundunar Operation Safe Haven da ke kunshe da jami’an sojoji, ‘yan sanda da ma civil defence ta samu nasarar cafke akalla mutum 100 da ake zargin sune suka jagoranci fasa dakin ajiyan kayan noma da ke unguwar dogon dutse, a Jos ta Arewa. Da safiyar yau aka wayi gari mutanen suka fasa dakin ajiyar wanda aka fi sani da PADP, inda suka kwashi buhunan takin zamani, janareto da sauran kayan da suke tare a dakin ajiyar.

Lamarin ya biyo bayan wanda ya afku jiya ne a karamar hukumar Jos ta Kudu, wato garin Bukuru; inda daruruwan jama’a suka yi warwason abincin tallafin cutar Korona da aka tara a wani babban dakin ajiya da ke kusa da kamfanin Nitel a garin na Bukuru. Hotona da suka hada dana bidiyo sun nuna yadda mutanen suka dinga warwason kayan abinci, wanda ya jawo gwamnatin jihar ta sanya dokar hana zirga-zirga a garuruwa Jos da Bukuru, amma duk da haka, wannan bai hana masu warwason su fita ba yau a garin Jos.

Zuwa yanzu ba a kai ga sanin mutum nawa aka cafke ba, amma a hotonan da rundunar OPSH ta saki na mutanen da ta cafke, an kama sama da mutum 100 da janareto da kuma buhunan takin zamani.

Exit mobile version