A yau Juma’a, mai magana da yawun rundunar sojojin ‘yantar da al’umma ta kasar Sin reshen gabashi Liu Runke, ya soki lamirin kasar Birtaniya, bisa yadda ta zuzuta abun da ya wakana yayin wucewar jirgin ruwan sintirinta ta zirin Taiwan a ranar Laraba.
Liu Runke, ya ce rundunar ta PLA reshen gabashi ta girke dakaru domin sanya ido ga yadda daukacin lamarin ya faru, tare da tabbatar da kasancewa cikin matakin koli na ko-ta-kwana, tare da aiwatar da matakai yadda ya kamata. (Saminu Alhassan)