Connect with us

LABARAI

Rundunar Soja Ta Karyata Sayar Da Filayen Bariki A Garin Warri

Published

on

Rundunar sojojin kasar nan ta ce, karya ce tsagwaron ta zargin da wani mai suna Mista Bictor Otomiebo yake  yi na cewar,rundunar sojoji sun sayar da filayen da aka shirya gina bariki a garin Warri ta jihar Delta.

Sanarwar data fito daga Daraktan watsa labaran rundunar sojojin Nijeriya Birgedia Tedas Chukwu, ya ce, zargin da aka yi wa rundunar sojojin Nijeriya da kuma shugaban sojojin Nijeriya, Janar Tukur Buratai a yayin gabatar da wani shirin talabiji na Channel mai suna “SUNRISE” ranar Asabar 2 ga watan Yuni 2018 karya ce tsagwaronta.

Chukwu ya kara da cewa, an yi amfani da wani bangaren filin ne wajen gina kasuwar barikin ‘Mammy Market’ yayin da aka kuma yi amfani da wani bangaren domin gina gidaje domin sojojin da suka yi ritaya daga bakin aiki a karkashin shirin samar wa tsaffin sojoji gida na “Post serbice housing estate.”

Ya ce, kanfanin sojoji mai suna “Nigerian Army Properties Limited (NAPL)” suka shiga yarjejeniya da kanfani mai suna “Chebron Employers Multi-purpose Cooperatibe Society Ltd” domn gina rukunin gidaje a wani bangaren filin da aka ware don gina wa tsaffin sojojin gidajensu. “Shugaban rudunar sojojin Nijeriya, Janar Tukur Buratai ba shi da hannun a kan yadda aka shiya yarjejeniyar da kuma yadda aka shirya sayar da hanunn jari Miliyan 50 a badakalar.”

“Babu wanda yake sayar wad a fararen hula filaye a kan Naira Miliyan 15 zuwa Miliyan 17, Janar Burutai kuma ba shi da fili ko shago a kasuwar na “Mammy Market,” inji Chukwu.

Daga nan rundunar sojojin ta bukaci Mista Bictor Otomiebo daya gabatar da shaidun zarge zargen da ya yi a cikin kwanaki 7 ko kuma ya shirya sauraran sammaci daga kotu.
Advertisement

labarai