Umar A Hunkuyi" />

Rundunar Soja Ta Karyata Zargin Da Gwamnan Ribas Ke Yi

Mazauna Kauye

Rundunar Sojin kasar nan ta musanta rahotannin da suke nuna cewa jami’anta sun yi yunkurin kashe Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike.
Cikin sanrwar da ta fitar a ranar Asabar da dare ta hannun Kakakinta, Musa Sagir, rundunar Sojin ta kwatanta rahoton da cewa, sam zuki ta malle ne.
An jiwo Gwamna Wike, yana sanar da yunkurin kisan na shi na kwanan nan ne a sa’ilin da ya karbi bakuncin tawagar kasar Ingila a gidan gwamnatin a ranar Juma’a.
A cewar rahoton, Gwamna Wike ya yi zargin Sojojin da suke aiki ne da babban Kwamandan bataliya ta 6, Manjo Janar Jamil Sarham, suka yi yunkurin kashe shi, a lokacin da suka kafa shinge a bisa hanyar da ta bi zuwa gidansa kafin zaben da aka daga a ranar 15 ga watan Fabrairu.
Rundunar ta mayar da martanin cewa, Gwamna Wike yana cikin damuwa ne na kasa samun nasarar yunkurin da ya yi ta yi na dusashe kimar rundunar Sojin.
A cewar sanarwar, rundunar Sojin tana zargin Gwamna Wike ne da neman yin batunci a kan jami’an Sojin.
Sanarwar ta kara da cewa, “Ba wani abu ne boyayye ba, shugabannin rundunar Sojin suna sane da yanda Gwamna Wike ya jima a lokuta da dama yana yunkurin bata sunan bataliyan ta 6. Ganin ya kasa cimma nasaran hakan ne duk da alkawurran milyoyin dalolin da ya rika yi mata shi a kashin kansa da kuma wasu na gewaye da shi, don haka bai zama da mamaki ba da gwamnan wanda ke cikin dimuwa ya koma yana kokarin yin bata sunan.”
“Mutum zai yi zaton irin matakin dagewa da rashin sabama gaskiyan da Manjo Janar Jamil Sarham, ya dauka duk da alkawurran dadadan abubuwan da aka yi ta yi masa, za su sanya ya sami yabo daga duk wani shugaba nagari. Amma sai ya kasance lamarin ba haka ba daga shi wannan gwamnan na Jihar Ribas, sai ma dai zargi marasa tushe.
Rundunar Sojin ta kalubalanci Gwamna Wike, ta kuma ba shi kwanaki bakwai da ya kawo shaidunsa a kan zargin da yake yi ko kuma ya daina yin irin wannan zargin marar tushe.

Exit mobile version